Saudiyya Ta Mika Kudurinta Na Neman Daukar Bakwancin Gasar Kofin Duniya A 2034

Saudiyya Ta Mika Kudurinta Na Neman Daukar Bakwancin Gasar Kofin Duniya A 2034

  • Kasar Saudiyya ta mika kudurinta na neman daukar bakwancin gasar cin kofin duniya a 2034
  • Hukumar kwallon kafa ta kasar ce ta sanar da haka a jiya Laraba 4 ga watan Oktoba
  • Wannan na zuwa ne bayan Qatar ta dauki nauyin gasar kofin duniya a shekarar 2022

Riyal, Saudiyya - Hukumar kwallon kafa a kasar Saudiyya ta sanar da mika kudurinta na neman daukar bakwancin kofin duniya na shekarar 2034.

Hukumar ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba.

Saudiyya na neman daukar bakwancin kofin duniya kamar Qatar
Saudiyya Na Neman Bakwancin Gasar Kofin Duniya. Hoto: Aljazeera.
Asali: AFP

Wane shiri Saudiyya ke yi na neman gasar kofin duniya?

Hukumar ta ce ta na fatan sauya bangarori da dama na kasar da ya shafi tattalin arziki da kuma wasanni saboda kofin duniya mafi kyau da za ta dauka, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

Sai An Zauna: Tsohon ‘Dan Majalisa Ya Yi Kira ga CBN Ganin $1 Ta Kai N1000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kudirin na zuwa ne bayan kasar Qatar ta dauki nauyin gasar a shekarar 2022.

Wannan ya bai wa kasar Qatar damar kafa tarihi na zama ta farko a Gabas ta Tsakiya da ta dauki bakwancin gasar a Nahiyar.

An bayyana Nahiyoyi uku da za su dauki nauyin gasar a shekarar 2030 wanda ya hada da kasashen Morocco da Sifaniya sai kuma Portugal, cewar Vanguard.

Amma kasashen Argentina da Uruguay da Paraguay za su karbi bakwancin wasanni daya-daya.

Wasu gasa Saudiyya za ta dauka nan gaba?

Masu fashin baki sun tabbatar da cewa siyan Christian Ronaldo na daga cikin shirye-shirye kan gasar kofin duniya na 2034.

Zuwan Ronaldo ya kara wa gasar Saudiyya armashi inda zaratan 'yan kwallo da dama su ka koma buga tambola a kasar.

Saudiyya har ila yau ta samu nasarar karbar bakwancin gasar cin kofin kasashen Asiya ta 2027.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Har ila yau, ita ce za ta karbi bakwancin gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin kwallon kafa da aka fi sani da Club World Cup.

Abubuwa 6 da Qatar ta yi na habaka Musulunci

A wani labarin, yayin da aka rufe gasar cin kofin duniya a Qatar, kasar ta yi bajinta wurin habaka addinin Musulunci.

Kasar ta kawo wasu tsare-tsare yayin gasar da aka yi wanda ya daga darajar Musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.