Abubuwa 6 da Qatar Ta Yi Da Suka Ɗaga Darajar Musulunci a Gasar Kofin Duniya 2022

Abubuwa 6 da Qatar Ta Yi Da Suka Ɗaga Darajar Musulunci a Gasar Kofin Duniya 2022

A yau Lahadi aka gudanar da bikin rufe gasar Cin Kofin Duniya 'Qatar 2022 FIFA World Cup a babban Filin wasan Lusail.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu matakai da ƙasar Qatar ta ɗauka domin kariya da kuma haɓaka Addinin Musulinci a kwanaki 28 na wasannin cin Kofin duniya.

Gasar cin Kofin duniya.
Abubuwa 6 da Qatar Ta Yi Da Suka Ɗaga Darajar Musulunci a Gasar Kofin Duniya 2022 Hoto: thenation
Asali: Twitter

Jerin abubuwa 6 da Qatar ta yi

1. Haramta sayar da Barasa a Filayen wasanni Takwas: Kwanaki biyu gabannin fara gasar, "Hukumar kwallon ƙafa ta duniya FIFA ta sanar da haramta sayar da Giya a filayen wasannin Qatar a Kofin Duniya."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

2. Gatar ta tsara Allunan sanarwa a jikin bango ɗauke da Hadisin Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata a gareshi) a birnin Doha gabanin fara wasanni.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan da Aka Fi Nema Ruwa a Jallo Ya Shiga Hannu

3. Ƙasar ta kuma sanya wasu alamomi a ɗakunan Otal Otal inda magoya bayan ƙungiyoyi zasu iya fahimtar Addinin Musulunci dai-dai da ra'ayoyinsu da Harsunansu.

4. Qatar ta sauya Ladanai masu kiran Sallah a Masallatai sannan ta kawo masu muryoyi masu daɗin sauraro. Haka nan an sanya Lasifiƙu a Filayen wasanni.

5. Cibiyar kula da baƙi ta ƙasar Qatar ta shirya masu wa'azi 2,000 waɗanda zasu kira mahalarta gasar zuwa Addinin Musulunci, ta ware musu motoci da Runfuna.

6. Daga ƙarshe, ma'aikatar Awqaf ta shirya haska Addinin Musulunci ga Baƙin da suka halarci gasar a Harsunan duniya daban-daban.

Haka nan kuma ta shirya wuraren yin Sallah da Alwala a filayen wasanni, ƙaro na farko a tarihin gasar cin kofin duniya.

‘Dan Gwamna Yayi Kira ga Hukumomin Qatar da Su Halaka Duk Wanda ya Shiga Filin Wasa da Giya

A wani labarin kuma Ɗan Gwamnan Kaduna Ya yi kira ga hukumomin Qatar da su ɗauki tsattsauran mataki kan duk wanda ya saɓa Dokar giya a filayen wasa

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Jiha Wuta, Sun Tafka Ɓarna

Bashir El-Rufai, ya ja hankalin masu amfani da kafafen sada zumunta yayin da ya nemi a halaka duk wanda aka kama da giya a filayen wasanni yayin Kofin Duniya.

Qatar dai ta ɗauki tsauraran matakai domin kaucewa saɓa wa Addinin Musulunci yayin kwanaki 28 da za'a yi ana fafatawa a gasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel