Dan Kwallon Ƙafan Najeriya Ya Mutu Bayan Yanke Jiki Ya Fadi A Filin Wasa A Jihar Arewa

Dan Kwallon Ƙafan Najeriya Ya Mutu Bayan Yanke Jiki Ya Fadi A Filin Wasa A Jihar Arewa

  • Wani matashin dan kwallo mai kwazo ya fadi ana tsaka da wasa kuma daga bisani ya ce ga garinku nan
  • Hukumar kwallon kafa ta Kogi ta bayyana mutuwar matashin a matsayin abin bakin ciki tare da yin jaje ga iyalansa
  • Matashin ya mutu ne bayan arangama da abokin wasansa kuma aka garzaya dashi asibiti inda ya mutu a can

Kogi - Wani matashin dan kwallo, Segun Idowu na kungiyar Barnet FC, Lokoja, Jihar Kogi, ya yanke jiki ya fadi bayan arangama da abokin wasansa kuma ya mutu daga bisani.

Lamarin ya faru ne ranar Juma'a lokacin da ake tsaka da gudanar da wasa a gasar da hukumar kwallon kafa ta Kogi ta shirya a filin wasa na Confluence, Lokoja, rahoton Daily Trust.

Taswirar Kogi
Dan Kwallon Kafan Najeriya Ya Mutu Bayan Yanke Jiki Ya Fadi A Filin Wasa. Hoto: Vangaurd
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ainihin mutanen da ke boye sabbin kudi, suna siyarwa a boye a Arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sanarwar da shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kogi, Alhaji Suleiman Isah Umar ya fitar, ya bayyana mutuwar bazata da matashin dan kwallon yayi a matsayin mutuwa mai radadi ga daukacin ma'abota kwallon kafar Kogi.

Ya ce gaba daya daukacin hukumar kwallon kafa ta Kogi ta shiga jimami bayan rasuwar matashin dan kwallo mai kwazo a ranar Juma'a.

Umar ya ce:

''Mun kadu matuka da safiyar nan da muka samu labarin mutuwar Segun, dan kwallon Barnet FC Lokoja, wanda ya fadi a filin wasa bayan arangama da abokin wasansa.
''Muna filin wasa lokacin da abin ya faru. An bashi taimakon gaggawa aka kuma garzaya dashi asibiti nan take. Rahoton da asibiti ya bamu shine yana samun lafiya kuma muka cigaba da rokon Allah ya bashi lafiya; kafin mu samu labarin komawarsa ga mahalicci.''

Kara karanta wannan

Saura ranar aiki 1 kacal, CBN Tace Ta Fitar Da Sabbin Kudi N120m Jihar Katsina

Umar ya kara da cewa:

''Daukacin ma'abota kwallon kafa a Lokoja sunji bakin cikin mutuwar matashin mai hazaka. Karamin karo ne kawai filin wasa, amma abun da ba taba tsammani ba hakan shine yayi sanadiyar komawar Segun ga mahalicci.
''Allah zai sanyawa ruhinsa salama ya kuma sanya dangana ga danginsa na kusa dana nesa a wannan lokacin na jimami; kuma muna addu'ar kada Allah ya kara maimata mana irin wannan lamarin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel