Ronaldo na Neman Mai Girki da Zai Dinga Biya N2,564,782.38 Duk Wata a Sabon Gidansa

Ronaldo na Neman Mai Girki da Zai Dinga Biya N2,564,782.38 Duk Wata a Sabon Gidansa

  • Fitaccen zakaran kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo, 'dan asalain Portugal, yana neman kwararren kuku a sabon gidan da yake tamfatsawa
  • Kwararren 'dan kwallon kafan zai dinga biyan kukun £4,500 wanda yayi daidai da N2,564,782.38 a kowanne watan duniya bayan an gama gidan
  • Sai dai, yana son a dinga ciyar da shi da matarsa tare da 'ya'yansa biyar da abincin Japan ne wadanda suka hadu kuma suka kasance masu dadi

Cristiano Ronaldo na fama da neman kwararren mai girki wanda zai dinga biya £4,500 wanda yayi daidai da N2,564,782.38 duk wata domin ya dinga ciyar da shi da iyalansa a gidansa na har abada a Portugal.

Cristiano Ronaldo
Ronaldo na Neman Mai Girki da Zai Dinga Biya N2,564,782.38 Duk Wata a Sabon Gidansa. Hoto daga mirror.co.uk
Asali: UGC

Kamar yadda mirror.co.uk suka bayyana, zakaran kwallon kafan na fama da matsalar samun kuku na kansa da iyalansa a katafaren gidan £17 million da yake ginawa a Portuguese Riviera.

Kara karanta wannan

Toh fa: Gwamna Wike ya fadi dan takarar da zai marawa baya a zaben 2023 mai zuwa

Katafaren gidan da za a kammala gina shi a watan Yuni, an gano nan zakaran kwallon kafan zai koma tare da iyalansa bayan ya daina kwallon kafa.

Wasu guraben ma'aikatan da ke da alaka da sabuwar fadar sun hada da sarkin gida wanda za a dinga biyansa £4,800 duk wata, wanda yanzu haka na samu amma ba a samu kuku ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zakaran kwallon kafan 'dan asalin kasar Portugal din an gano cewa ya tsara katafaren gidan nasa ne da tsarin kuku ya kasance mai dafa abincin Japan.

Sai dai tambayar ita ce, waye zai dinga dafa masa sushi da sauran ciye-ciyen kasar tare da Rodriguez da yaransa biyar? Hakan na matukar ci masa tuwo a kwarya.

Ronaldo wanda a cikin watan nan a hukumance ya sama zakaran kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr bayan sa hannu da suka yi kan kwantiragin shekara daya, ya kasa samun hadadden mai girkin da zai share masa hawaye duk da makuden kudin da ya ware zai dinga biya duk wata.

Kara karanta wannan

Kamar Almara: Dan Wasan Da Ya Fi Kowa Kokari a Wasan Kwallo Ya Samu Kyautar Kwai

Hotunan cikin katafaren otal din da Ronaldo ke zama tare da iyalansa a Saudi Arabia

A wani labari na daban, Ronaldo da masoyiyarsa tare da yaransa biyar suna zama a wani katafaren otal da ke kasar Saudi Arabia bayan sa hannu da yayi da kungiyar Al-Nassr na kwantiragin shekara daya.

Sun zama ne a wurin da ya kunshi dakunan bacci har 17.

Asali: Legit.ng

Online view pixel