Dan Wasa Ya Samu Kyautar Kiretan Kwai 5 Bayan Ya Lashe Gasar Kwallon Kafa

Dan Wasa Ya Samu Kyautar Kiretan Kwai 5 Bayan Ya Lashe Gasar Kwallon Kafa

  • Wani jarumin kwallon kafar kasar Zambiya wanda ya nuna bajinta yayin wani wasa da suka buga da abokan karawarsu ya samu kyauta ta musamman
  • An yi wa Kennedy Musonda na kungiyar Power Dynamos kyautar kiretan kwai guda biyu bayan ya zura kwallo daya tilo da aka ci a wasan
  • Musonda ya samu karin kiretan kwai uku na zama gwarzon wasan da suka buga a karshen makon jiya

Zambiya - A wani lamari mai kama da al’amara, an baiwa wani dan kwallon kafar kasar Zambiya kiretan kwai guda biyar bayan ya zama zakaran gwajin dafin wani wasa da suka buga.

Kennedy Musonda, dan wasan kwallon Zambiya da ya buga wasan gaba ya samu karramawa saboda namijin kokarin da ya yi a wasan da suka buga a karshen makon jiya.

Yan wasa da kwai
Dan Wasa Ya Samu Kyautar Kiretan Kwai 5 Bayan Ya Lashe Gasar Kwallon Kafa Hoto: Teller Report
Asali: UGC

Kennedy ne ya zura kwallo daya tilo da aka ci a wasan da aka buga tsakanin Power Dynamos da abokan hamayyarsu, Nkana Football Club.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

Rahotanni daga Zambia sun ce an ba shi kiretan uku saboda kasancewarsa ‘zakaran gwajin dafin wasan’, yayin da aka bashi karin kiretan kwai biyu kan kwallon da ya zura a raga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani masoyin kulob din da ke da gonar kaji shine ya gabatarwa Kenny Musonda kiretan kwan.

Zuwa yanzu, dan wasan mai shekaru 27 ya zura kwallaye shida ga bangarensa a wannan kakar.

Shafin @TrollFootball ma ya wallafa hotunan dan wasan yana karbar kyautarsa a Twitter inda jama'a suka tofa albarkacin bakunansu.

Martanin jama'a

@wbulime ya yi martani:

"Afrika tamu. Yan wasan kwallon kafa na son ciye-ciye."

@Nicolaj_Gericke ya ce:

"Na taba lashe kyautar madara, idan aka hada da wannan zai haifar da hadadden cincin mai dadi."

@a_tanudjaja ya ce:

"Tamkar gwal ne yadda farashin yake a yanzu."

Bidiyon wasu kyawawan jami'an soji ya ta da kan yan maza

Kara karanta wannan

Sai a kula: Kudaden bogi na kara yawa, mai POS ya ba da N1000 na bogi, an ki karba a kasuwa

A wani labari na daban, mun ji cewa bidiyon wasu jami'an sojoji mata biyu ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya inda samari suka mato a kansu saboda tsantsar kyawun da Allah ya yi masu.

An dai gano sojojin biyu wadanda ke aiki tare da rundunar sojin Amurka sanye da inifam dinsu yayin da suke taka rawa tare da rera wakar shahararren mawakin Najeriya, Davido.

Asali: Legit.ng

Online view pixel