Hotunan Cikin Katafaren Gidan da Ronaldo, 'Ya'Yansa da Budurwarsa Suke Zaune a Saudi Arabia

Hotunan Cikin Katafaren Gidan da Ronaldo, 'Ya'Yansa da Budurwarsa Suke Zaune a Saudi Arabia

  • Fitaccen zakaran kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo, yana zama a wani katafaren otal tare da 'ya'yansa da budurwarsa da suke rayuwa tare a kasar Saudi Arabia
  • An gano cewa, iyalan na zama ne a wuri mai dakuna 17 inda ake biyan euro 284,000 a kowannen wata bayan saka hannun kan kwantiraginsa da Al-Nassr
  • Nan babu dadewa, zai koma wani katafaren gida mai darajar 12 miliyan euro a kasar Saudi Arabia, ga wasu hotunan otal din da yake a yanzu

Saudi Arabia - Shahararren 'dan wasan kwallon kafan da yayi shuhura a duniya, Cristiano Ronaldo, wanda yasa hannun kan kwantiragin shekara biyu da rabi mai darajar £177 miliyan duk shekara da Al-Nassr, yanzu haka yana zaune a daya daga cikin otal mafi kyau a kasar Saudi Arabia.

Ronaldo
Hotunan Cikin Katafaren Gidan da Ronaldo, 'Ya'Yansa da Budurwarsa Suke Zaune a Saudi Arabia. Hoto daga Marca.com
Asali: UGC

Tsohon zakaran Machester United din ya koma kasar Saudi Arabia tare da Rodriguez, budurwarsa wacce suke zama tare da 'ya'yansu biyar.

Duk da haramcin zama tare tsakanin wadanda ba su yi aure ba a kasar, rahotanni sun bayyana cewa hukumomin za su daga musu kafa kan wannan dokar.

Marca.com, wata yanar gizo da ke kawo labarun wasanni sun kawo wasu hotunan katafaren otal din da ke Riyadh, babban birnin Saudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ronaldo da iyalansa za su dinga zama a dakuna 17 a otal din mai matukar kayatarwa kan euro 284,000 a kowanne wata.

Za su zauna a otal din mai hawa biyu kafin su koma katafaren gidansu mai darajar euro miliyan 12 kamar yadda shafin yanar gizon ya bayyana.

Ga wasu daga cikin hotunan:

Ronaldo
Hotunan Cikin Katafaren Gidan da Ronaldo, 'Ya'Yansa da Budurwarsa Suke Zaune a Saudi Arabia. Hoto daga marca.com
Asali: UGC

Ronaldo
Hotunan Cikin Katafaren Gidan da Ronaldo, 'Ya'Yansa da Budurwarsa Suke Zaune a Saudi Arabia. Hoto daga marca.com
Asali: UGC

Ronaldo
Hotunan Cikin Katafaren Gidan da Ronaldo, 'Ya'Yansa da Budurwarsa Suke Zaune a Saudi Arabia. Hoto daga marca.com
Asali: UGC

Ronaldo
Hotunan Cikin Katafaren Gidan da Ronaldo, 'Ya'Yansa da Budurwarsa Suke Zaune a Saudi Arabia. Hoto daga marca.com
Asali: UGC

Saudi ta lankwasa dokarta saboda Ronaldo

A wani labari na daban, kasar Saudi Arabia ta tankwara dokarta saboda shahararren 'dan wasan kwallon kafa na duniya wanda kwanan nan kungiyar kwallon kafa ta kasar, Al-Nassr ta siye shi.

A dokar kasar, matukar mace da namiji ba su yi aure ba, ba su da samar zama tare kuma ana hukunta su idan aka kama hakan.

Sai dai ba hakan za ta kasance ga shahararren 'dan wasan kwallon ba da yake zama tuni da masoyiyarsa wacce suke da 'ya'ya tare amma ba su taba yin aure ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel