Cristiano Ronaldo da Ragowar ‘Yan wasa 10 da Suka fi Kowa karbar Albashi a 2023
- Tauraron kungiyar Al Nassr, Cristiano Ronaldo ya zama ‘dan wasan da ya fi kowa albashi a yau
- ‘Dan kwallon ya yi goshi ne bayan ya koma buga wasa a kasar Saudi Arabiya bayan barin Ingila
- A bayan ‘dan wasan akwai, Lionel Messi, Neymar Jr da suke bugawa kungiyar PSG a Faransa
Spain - Marca a wani rahoto da ta fitar a karshen makon nan, ta tattaro ‘yan wasan da albasinsu ya sha gaban kowa a Duniya.
Na farko a jerin shi ne ‘dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo wanda kungiyar Al Nassr ta dauke shi a cikin shekarar bana.
A jerin akwai ‘yan wasan kwallon kafa, ‘yan wasan American Football da kuma wadanda suka yi suna wajen yin tseren mota.
1. Cristiano Ronaldo
‘Dan wasan gaban kasar Portugal, Cristiano Ronaldo zai samu €112.1m a Saudi Arabia, ‘dan wasan mai shekara 37 bai da sa’a wajen karbar albashi mai tsoka a yau.
2. Lionel Messi
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Duk inda aka ji Ronaldo, za a kira Lionel Messi na kasar Argentina. Tauraron zai samu €70.6m a kungiyar PSG da ya koma bayan ya bar Barcelona a bara.
3. Neymar
Rahoton DBRS Morningstar da SportBible sun nuna Neymar da Silva Santos Júnior ne na uku. ‘Dan kwallon na Brazil zai samu €65.9m a Paris Saint-Germain.
4. Matthew Stafford
John Matthew Stafford yana buga wasan American Football ne da kungiyar Los Angeles Rams. Albashisa ya kai €65.7m, da kadan Neymar ya sha gaban shi.
5. Josh Allen
Shi ma Joshua Patrick Allen abokin aikin John Stafford ne da yake bugawa kungiyar nan ta Buffalo Bills a Amurka, ana lissafin albashinsa a yanzu ya kai €59.3m.
6. Aaron Rodgers
Rahoton ya ce Aaron Charles Rodgers mai albashin €53.7m a Green Bay Packers yana cikin jerin attajiran ‘yan wasan a 2023, shi ma tauraron ‘American Football’ ne.
7. Lewis Hamilton
Lewis Carl Davidson Hamilton ya yi kudi ne da Formula One. Direban marsandin da ya zo na farko a Duniya sau bakwai yana karbar €53.7m a matsayin albashi.
8. Deshaun Watson
Kungiyar Cleveland Browns ta na biyan €52.3m ga Derrick Deshaun Watson a shekara. Wannan ya sa yake cikin ‘yan wasan da kudinsu ya fi na kowa yau.
9. Kirk Cousins
‘Dan wasan ‘American football’ na karshe a sahun goman farko shi ne Kirk Daniel Cousins da yake bugawa Minnesota Viking. Ana maganar yana tashi da €43.3m.
10. Max Verstappen
Baturen ‘dan wasan tseren motan nan, Max Emilian Verstappen yana samun albashin da ya kai €43.3m da Red Bull Racing wajen gasar nan na Formula One.
Faiq Bolkiah bai da na 2
Ku na da labari kusan Naira Biliyan 30 Cristiano Ronaldo zai rika karba a matsayin albashin shekara a Al Nassr, duk da haka akwai ‘dan kwallon da ya fi shi kudi.
An taba yin lokacin da a duk wata sai ‘dan wasan kwallon kafan nan, Faiq Bolkiah ya yi facaka da kimanin Naira Biliyan 20, a duk 'yan kwallo babu mai dukiyarsa.
Asali: Legit.ng