Mikel Obi, Tsohon Kyaftin Din Super Eagles, Ya Yi Murabus Daga Kwallon Kafa

Mikel Obi, Tsohon Kyaftin Din Super Eagles, Ya Yi Murabus Daga Kwallon Kafa

  • Fitaccen tauraron dan kwallon Najeriya, Mikel Obi ya sanar da cewa ya yi murabus daga kwallon kafa
  • Tsohon dan wasan na kungiyar Chelsea ya bayyana hakan ne a ranar Talata a shafinsa na dandalin sada zumunta
  • Obi ya ce komai da ke da farko dama yana da karshe kuma ya gamsu da irin nasarori da darussan da ya koyi cikin shekaru 20 na buga kwallo

Tsohon Kyaftin din Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, Mikel Obi ya yi murabus daga wasan kwallon kafa bayan shekaru 20 yana wasan.

Tsohon dan wasan Najeriyan ya sanar da murabus dinsa na a shafinsa na soshiyal midiya a ranar Talata.

Mikel Obi
Mikel Obi Ya Yi Murabus Daga Kwallon Kafa. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

Obi ya yi murabius yana da shekaru 35 a duniya bayan cin lambobin yabo ga kasarsa Najeriya kungiyoyin da ya buga wa wasa.

Kara karanta wannan

Mai kamar maza: Bidiyon budurwa mai tuka tirela ya girgiza intanet, jama'a sun shiga mamaki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon tauraron na Chelsea ya ce:

"Akwai karin magana da cewa duk 'duk dadin abu yana ranar karewa' kuma a matsayi na na dan kwallon kafa, yau ne ranar.
"Na yi waiwaye kan shekaru 20 da na yi ina wasan kwallo, kuma ba abin da zan ce shine na gamsu da nasarorin da na samu kuma mafi muhimmanci yadda ta taimaka min saita rayuwa na."

Tsohon kyaftin din na Super Eagles ya kuma mika godiyarsa ga cocinsa, iyalansa, magoya baya, masoya da takwarorinsa.

Ya ce:

"Kun karfafa min gwiwa a kowanne hali da na shiga, har a ranakun da ban yi abin da kuke tsammani ba, ina mika godiya sosai."

Ya cigaba da cewa ba bankwana ya ke yi ba, sai dai zai fara wani sabon shafi ne a rayuwarsa kuma yana fatan mutanen da ke rayuwarsa za su cigaba da kasancewa tare da shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sakamakon Rikici, An Dakatad Da Fara Kamfen APC Sai Baba Ta Gani

Kungiyar Chelsea ta yi wa Obi fatan alheri

Kungiyar Chelsea, a sahihin shafinta na Twitter ta yi wa Obi fatan alheri a yayin da ya yi murabus daga kwallo.

Likitan CAF Ya Yanke Jiki Ya Faɗi Bayan Wasar Najeriya Da Ghana, Akwai Yiwuwar a Hukunta Najeriya

A wani rahoton, wani likita da ke aiki da kungiyar wasan kwallon kafar nahiyar Afirka, CAF, Dr. Joseph Kabungo ya mutu jim kadan bayan Ghana ta cire Najeriya a gasar kwallon kafa da aka yi ranar Talata, 29 ga watan Maris.

Kabungo, likita ne dan asalin kasar Zambia, kuma ya mutu ne bayan wani cunkosu ya auku a filin wasan Moshood Abiola da ke Abuja kafin a fara wasan, Legit.ng ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164