Jihar Zamfara
Dakarun sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara. A yayin artabun an kashe 'yan bindiga masu yawa yayin da aka samu asarar rayukan wasu sojoji.
Wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun yi basaja wajen satar mutane a jihar Zamfara. Miyagun sun zo da sabon salo yayim da suka sace bayin Allah zuwa cikin daji.
An kama mutane 6 cikin wandanda ake zargi da kai hari wani masallaci ana sallar asuba a jihar Zamfara. Maharan sun tafi da wasu masallata yayin harin.
Mazauna Arewacin Zamfara sun nuna damuwa kan daukewar sabis na sadarwa a kananan hukumominsu, sun roki hukumar NCC ta shiga tsakani don dawo da sabis.
A labarin nan, za a ji yadda jama'a su ka gamu da iftila'in harin 'yan bindiga a jihar Zamfara a wani harin ba zata da 'yan bindiga su ka kai zuwa Gusau.
Kungiyar 'Zamfara Good Governance Network' ta soki gwamna Dauda Lawal na Zamfara kan cewa zai iya dakile ta'addanci a mako biyu inda ta zarge shi kan makarkashiya
Rahotanni sun tabbatar da cewa jagoran yan ta'adda, Kachalla Abu Dan Barka, da wasu mayaƙansa huɗu sun mutu a harin abokan gaba a karamar hukumar Maru, Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar da cewa fada tsakanin kungiyoyin yan bindiga ya zama silar kashe jagorori biyu, Kachalla Mai Hidima da Kachalla Bingil a Zamfara.
Jagoran 'yan bindiga a jihar Zamfara, ya fusata inda ya bindige wasu daga cikin mayakansa. Ado Aleiro ya yi kisan ne da kansa kan zargin cin amana.
Jihar Zamfara
Samu kari