Siyasar Najeriya
Mai neman zama shugaban kasa a inuwar New Nigerian Peoples Party, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara yakin neman zaben NNPP a jihar Bauchi, arewa maso gabas.
Mai magana da yawun jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara, Yusuf Idris, ya karyata rahoton da ke yawo cewa na gaban goshin Matawalle sun sauya sheka zuwa PDP.
Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar African Democratic Congress, Dumebi Kachikwu, ya bayyana cewa an gwada shi ya kamu da cutar Korona, ya killace.
Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, kodinetan matasa yace lokacin kawai suke jira su raka Bola Ahmed Tinubu fadar shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Jam'iyyar Labour ta jihar Bayelsa ta cire shugaban ta na jihar, Eneyi Zidough saboda zarginsa da almubazaranci da kudi, saba dokokin jam'iyya da wasu laifukan.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi sabbin jakadun kasashen waje cewa kada su yi katsalandan a babban zaben 2023, ya ce su yi aikinsu bisa kwarewa da bin doka.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano ya ja kunnen Gwamna Ganduje da babbar murya kan yi masa zagon kasa a zaben 2023 mai zuwa, yace zai yi matukar nadama.
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bawa yan Najeriya shawarwari kan shugaban kasar da ya dace su zaba a 2023, ya ce dole ya fahimci tattalin arziki.
Yanzu muke samun labarin cewa, dan takarar shugaban kasa na PDP ya dawo gida Najeriya bayan da ya shafe kwanaki yana can a Landan. An fadi me ya kai Landan.
Siyasar Najeriya
Samu kari