2023: Hantar PDP, Atiku Ta Kada Yayin Da Yar Tinubu Ta Ziyarci Babban Dattijon Arewa, Bayanai, Hotuna Sun Fito

2023: Hantar PDP, Atiku Ta Kada Yayin Da Yar Tinubu Ta Ziyarci Babban Dattijon Arewa, Bayanai, Hotuna Sun Fito

  • Yayin da jam'iyyar hamayya ta PDP ke fama da rikicin cikin gida, jam'iyyar All Progressives Party, APC, mai mulki a kasa na cigaba da aiki don ganin ta yi nasara
  • Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Party, APC ba ya kasa a gwiwa don ganin ya zama shugaban kasa na gaba
  • Wannan shine dalilin da yasa sansanin na Tinubu ke cigaba da kokarin kamun kafa gaba da Atiku Abubakar da Peoples Democratic Party, PDP, musamman a yankin arewa

Jihar Kano - Mrs Folashade Tinubu-Ojo, Iyaloja Janar, yar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Party, APC, ta ziyarci dattijon arewa, Alhaji Tanko Yakasai.

Yayin ziyara, yan siyasar biyu sun dauki lokaci sun yi tattaunawa mai amfani a tare.

Tanko Yakasai
2023: Hantar PDP, Atiku Ta Kada Yayin Da Yar Tinubu Ta Ziyarci Babban Dattijon Arewa, Bayanai, Hotuna Sun Fito. Hoto: Tinubu Campaign Group
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Gamu Da Taskun Matasan Yankinsa, Inda Suka Zargeshi Da Yin Watsi Da Su

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalilin kai ziyarar

Dan sa kuma jagora na kasa, Umar Tanko Yakasai da wasu shugabanin jam'iyyar All Progressives Party, APC, ne ya yi mata jagora, The Nation ta rahoto.

Mrs Tinubu ta tabbatarwa dattijon na kasa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin cewa Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya yi nasara.

A jawabinta na rufewa, ta zaburar da kungiyoyi su tabbatar sun janyo mata a jiki a harkokinsu a wani mataki na karfafawa mata gwiwa su shiga siyasa da daidaito tsakanin jinsi a kasa.

Ta yaya hakan zai shafi Atiku

Yana da muhimmanci a sani cewa tunda har yanzu jam'iyyar PDP ba ta riga ta sulhunta kanta ba, APC na amfani da wannan dama a kowanne lokaci da ta samu.

Gabanin babban zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyar APC na cigaba da kokarin kamun kafa musamman a yankin arewa, tana tuntubar dattawa, kuma hakan na iya shafar damar nasarar jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasarta a zaben da ke tafe don samar da wanda zai maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bidiyo ya fito, Atiku ya dawo daga Landan tare da wasu jiga-jigan PDP

2023: Asiwaju Tinubu ya samu sarautar gargaziya a Ebonyi

A bangare guda, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya samu sarautar gargajiya a jihar Ebonyi.

An nada tsohon gwamnan na Legas wannan sarautar ta 'Dike Di Ora Nma I' a jihar Ebonyi ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamban 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel