Jam'iyyar NNPP Ta Zama Babbar Jam'iyyar Adawa a Majalisar Gombe

Jam'iyyar NNPP Ta Zama Babbar Jam'iyyar Adawa a Majalisar Gombe

  • Jam'iyyar Kwankwaso ta zama babbar jam'iyyar marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Gombe bayan kara samun tagomashi
  • Mamba mai wakiltar mazabar Kantungo ta yamma, Bashir Yakubu Barau ya tattara kayansa daga APC ya koma NNPP
  • Wannan ci gaba ya baiwa NNPP damar samun yan majalisu hudu a zauren, ta haura PDP mai guda uku

Gombe - New Nigerian Peoples Party (NNPP) ta zama babbar jam'iyyar marasa rinjaye a majalisar dokokin jihar Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoton cewa hakan ya biyo bayan sauya shekar mamba mai wakiltar mazabar Kaltungo ta yamma, Bashir Yakubu Barau, wanda ya shiga NNPP bayan barin APC mai mulki.

Majalisar dokokin jihar Gombe.
Jam'iyyar NNPP Ta Zama Babbar Jam'iyyar Adawa a Majalisar Gombe Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Barau ya samu kyakkyawar tarba daga dan takarar gwamnan jihar Gombe a inuwar NNPP, Khamisu Ahmad Mailantarki.

Kafin wannan ci gaban, jam'iyyar PDP da NNPP na da mambobi uku uku daga cikin yan majalisar jiha 24 da Suka hada majalisar dokokin Gombe.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Gamu Da Taskun Matasan Yankinsa, Inda Suka Zargeshi Da Yin Watsi Da Su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma bayan sauya shekar Barau, a yanzu NNPP na da mambobi hudu a zauren majalisa kuma haka ya ba ta damar zama jam'iyar babbar jam'iyar adawa.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoto a kwanakin baya cewa mambobin majalisa 2 daga APC da ɗaya daga PDP sun sauya sheka zuwa kayan marmari.

Meyasa dan majalisar ya zabi komawa NNPP?

Da yake jawabi ga manema labarai, Barau yace ya shiga NNPP ne saboda kaunar jiharsa, inda ya kara da cewa APC da PDP ba su da kwarewar da zasu kawo sauyin cigaba a Gombe.

Tun bayan ayyana Mailantarki a matsayin dan takarar gwamna na NNPP, fusatattun mambobin APC da PDP ke ci gaba da tururuwa suna komawa mai alamar kayan marmari.

Ko a yan kwanakin nan, tsoffin mataimakan shugaban karamar hukuma hudu a Billiri, Kwami, da Nafada tare da tsohon Kansila suka fice daga PDP zuwa NNPP.

Kara karanta wannan

2023: APC tayi babban rashi, mataimakin kakakin majalisar Kaduna da Wani Mamba Sun Sauya Sheka

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya sake tunawa jam'iyyar PDP damarta ta karshe ta nemi sulhu da tawagar G-5

Gwamna Nyesom Wike yace har yanzun PDP na da damar neman sulhu da gwamnonin G-5 kafin su bayyana dan takarar da zasu marawa baya.

Wike, jagoran G-5 da ta balle daga PDP yace idan suka rufe kofa, suka zabi wanda suke so, ko sama da kasa zata haɗe ba wanda ya isa ya hana su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel