Zaben 2023: Tinubu Ne Shugaban Kasa Mai Jiran Gado, Yahaya Bello

Zaben 2023: Tinubu Ne Shugaban Kasa Mai Jiran Gado, Yahaya Bello

  • Kodinetan Matasa na kwamitin kamfen APC yace lokaci ne alkali, Bola Tinubu ne shugaban kasa mai jiran gado
  • Gwamna Yahaya Bello yace Tinubu kaya ne mai kyau da ya riga ya sayar da kansa ga yan Najeriya kafin ranar zabe
  • Gwamna Bello ya kai ziyara ga shugaban ƙasa Buhari domin gode masa bisa zuwa da kansa ya kaddamar da ayyuka a Kogi

Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, yace dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ne, "Shugaban kasa mai jiran gado."

Gwamnan Bello, Kodinetan matasa na kwamitin kamfen Tinubu/Shettima, ya fadi haka ne ranar Jumu'a bayan gana wa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Tinubu da Yahaya Bello.
Zaben 2023: Tinubu Ne Shugaban Kasa Mai Jiran Gado, Yahaya Bello Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

The Cable tace Gwamnan ya kai wa Buhari ziyara ne domin gode masa da kuma gabatar masa da kunshin Hotunan ayyukan da ya kaddamar a ranar 29 ga watan Disamba, 2022 a Kogi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Osun Ya Fadi Abin da Za a Rika Tuna Buhari da Shi Bayan Mayun 2023

Da yake zantawa da yan jaridan gidan gwamnati, Bello yace Bola Tinubu kaya ne mai inganci wanda ya riga ya sayar da kansa domin samun kuri'un 'yan Najeriya ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan ya jaddada cewa zasu, "Raka shi zuwa cikin fadar shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, 2023 cikin farin ciki da idan Allah ya so," kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yayin da aka tambaye shi kan damar dan takarar APC ke da su a zabe mai zuwa duba da yadda ya karade kasa yana tallata shi, gwamna Bello ya ce:

"Tinubu na tare da gwamnoni 21 na APC, Tinubu ya taba rayuwar 'yan Najeriya a kowane yanki, ya gina kasa. Shi mai gina wa ne, ya gina mutane sun kafu kuma ya gina kasa, kuma ya soma fada mana abinda zai aikata."

Kara karanta wannan

2023: Magana Ta Kare, Bola Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Ana Gab da Zabe

"Gwamnatinsa da ikon Allah matasa ne zaku gani a sahun gaba kuma abinda baku sani ba wadan nan matasan sun kunshi wani adadi na masu kada kuri'a a zabe mai zuwa."
"Mun san Bola Tinubu ya san hanya kuma mun shirya tsaf na bin bayan mutumin da ya san hanya. mun gode Allah shi ne dan takarar Buhari."

Buhari Ya Gana da Dan Takarar Gwamnan Abiya Na APC

A wani labarin kuma Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya ɗaga hannun dan takarar gwamnan Abiya na jam'iyyar APC a Aso Rock

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kebe da dan takarar gwamnan Abiya a inuwar APC, Ikechi Emenike da matarsa a Aso Villa.

Buhari ya tabbatar da goyon bayansa ga dan takaran kuma ya ɗaga masa hannu. An ba Buhari kyautar zanen Hotonsa a 2012.

Asali: Legit.ng

Online view pixel