Jam'iyyar APC Ta Musanta Rahoton Cewa Hadiman Gwamna Matawalle Sun Koma PDP

Jam'iyyar APC Ta Musanta Rahoton Cewa Hadiman Gwamna Matawalle Sun Koma PDP

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta karyata rahoton da ke cewa manyan hadiman Matawalle ne suka koma PDP
  • A wata sanarwa da PDP ta fitar, ta yi ikirarin cewa mashawartan Matawalle uku sun sauya sheka daga APC
  • Kakakin APC a Jihar, Yusuf Idris, ya fito ya fayyace gaskiya tare da bayar da hujjoji kan wadanda suka koma PDP

Zamfara - Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta musanta rahoton dake yawo cewa manyan hadiman gwamnan Bello Matawalle guda uku sun sauya sheka zuwa PDP.

APC ta bayyana cewa rahoton wanda yan midiyan gidan PDP suka kirkira cewa mashawarta na musamman uku da Matawalle ke ji da su sun bar APC karya ne.

Masu sauya sheka a Zamfara.
Jam'iyyar APC Ta Musanta Rahoton Cewa Hadiman Gwamna Matawalle Sun Koma PDP Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa a wasu sanarwa biyu daban-daban da PDP ta fitar, ta ce makusantan gwamnan ba su gamsu da salon mulkin Matawalle ba shiyasa suka kama gabansu.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso ya fadi yadda zai sauya tsarin JAMB, NECO da WAEC idan ya gaji Buhari

"Tsohon shugaban APC a Zamfara, mataimakin sakataren tsare-tsare na APC a shiyyar Zamfara ta tsakiya, Alhaji Musa Malalla sun koma PDP don marawa Dauda Lawal baya," inji PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata sanarwan ta daban ta ce:

"Guguwar sauya sheka ta turnuke APC mai mulki a Zamfara yayin da masu baiwa gwamna shawara na musamma har guda uku suka koma PDP. Dan takarar Gwamna, Dauda Lawal ne ya karbe su a gidansa."

Karya ce tsanta inji APC

A ruwayar Punch, yayin da take martani, jam'iyyar APC ta bakin mai magana da yawunta, Yusuf Idris, ya ce wadan da suka sauya shekar ba su da kusanci da gwamna Matawalle.

Yace mutanen guda uku, Hamisu Magami, Abubakar Maigandi da Yunusa Rosy, sun rike mukamin ne a mulkin tsohon gwamna, Abdul'aziz Yari.

Idris ya kara da cewa Garba Muhammad Danburan, tsohon shugaban hukumar zabe ta jiha (ZASIEC) ne amma ba shugaba mai ci ba kamar yadda PDP ta yi ikirari.

Kara karanta wannan

"Allah Ya Tona Maka Asiri" Gwamnan Arewa Ya Maida Zazzafan Martani Ga Tsohon Mataimaki Da Ya Koma PDP

Kakakin APC ya bayyana rahoton da gurbatacce kuma karya ce mara tushe. Idris ya ce:

"Rahoton baki ɗayansa gurbatacce ne kuma wani shiri ne da PDP ta kirkiro tare da masu sauya shekan na rufa-rufan kanzon kurege. Yana da kyau mu share waswasin yan Najeriya domin Zamfarawa sun san komai."
"Mutane ukun da aka ce hadiman gwamna ne karya ne. Sun rike mukaman masahawarta ne a zamanin mulkin tsohon gwamna, Abdul'Aziz Yari. Ba su da gurbi a mulkin Matawalle."

Dan takara a 2023 ya kamu da Korona

A wani labarin kuma kun ji cewa Dan Takarar Shugaban Kasa, Kachikwu, Ya Kamu Da Cutar Korona

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya kamu da cutar Korona Birus.

A wata sanarwa jiya Jumu'a, dan takarar yace ya killace kansa, ya roki mutane su kula domin watakila Annobar ta dawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel