Dan Takarar Shugaban Kasa, Kachikwu, Ya Kamu Da Cutar Korona

Dan Takarar Shugaban Kasa, Kachikwu, Ya Kamu Da Cutar Korona

  • Mai neman zama shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya kamu da cutar Koroma Birus
  • A wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, Kachikwu ya bayyana cewa ya killace kansa har sai an tabbatar masa da ya warke
  • Ya yi kira ga yan Nqjeriya da su ci gaba da bin matakai suna zuwa ana gwada su domin kar a maida hannun agogo baya a Najeriya

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress, Dumebi Kachikwu, a ranar Jumu'a ya bayyana cewa ya kamu da cutar Covid-19 wato Korona.

Mista Kachikwu ya yi kira ga 'yan Najeriya su yi takatsantsan domin akwai yuwuwar cutar ta sake dawowa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Dumebi Kachikwu.
Dan Takarar Shugaban Kasa, Kachikwu, Ya Kamu Da Cutar Korona Hoto: punchng
Asali: UGC

Mai neman kujera lamba daya a Najeriya a inuwar ADC ya fadi haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a 13 ga watan Janairu, 2023.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Buhari, Gwamna Ya Bayyana Shugaban Kasa Mai Jiran Gado a 2023

A sanarwan, Kachikwu ya bayyana cewa tuni ya killace kansa kuma ya soke duk wasu tarukan al'umma har zuwa lokacin da za'a tabbatar masa ya warke daga cutar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma kara da kira ga mutanen Najeriya karsu dauki lamarin Korona da wasa domin a halin da ake ciki adadin masu kamuwa da ita ya karu a fadin duniya a cikin makonnin nan.

A rahoton Vanguard, Dan takarar shugaban ƙasan ya ce:

"Bai kamata 'yan Najeriya su jingine matakan kariya ba duk da gwamnati ta sassauta dokokin COVID19, tsarin kula da lafiyarmu ba zai iya daukar yawaitar kamuwa da cutar ba."
"A yanzu muna wani lakaci da kwararrun likitoci ke barin kasa, ya kamata mu rika zuwa ana gwada mu kuma mu bi matakan dakile yaɗa cutar. Dole mu guje maida ralin kamfe wurin yada korona, kar mu maida hannun agogo baya."

Kara karanta wannan

Assha: Ba a gama da jimamin Hanifa ba, wasu matasa sun sace yarinya mai shekaru 6 a Kano

"Zamu fita daga annobar Korona idan har muka natsu kuma muka bi matakan da ya dace."

Kungiyoyin ƙwadugo sun zabi Tinubu

A wani labarin kuma Bola Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Ana Gab da Zabe a watan Fabrairu mai zuwa

Kungiyoyin kwadugo a jihar Legas sun bayyana goyon bayansu ga kudirin Bola Ahmed Tinubu na zama shugaban kasa a babban zaben 2023.

A wani babban rali da suka shirya a Ikeja, kungiyoyin sun kuma ayyana cewa suna tare da gwamna Sanwo-Olu ya ci gaba da mulkin Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel