Saura Kwanaki Kadan Zabe, Kwankwaso Ya Aike da Jan Kunne da Kakkausar Murya ga Ganduje

Saura Kwanaki Kadan Zabe, Kwankwaso Ya Aike da Jan Kunne da Kakkausar Murya ga Ganduje

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, 'dan takarar kujerar shugaban kasa a NNPP, ya ja kunnen Gwamna Ganduje kan yi masa zagon kasa a zaben 2023
  • Kwankwaso yace matukar ya ci zaben shugaban kasa, Kano ce ta farko da za ta fi mora sai arewacin Najeriya da kasar baki daya a sanin da aka yi masa
  • Ya tabbatar da cewa, ralin da yayi a wasu sassan Kano babu wanda zai iya yin kamarsa saboda wasu aro jama'a suke daga makwabtan jihar don gangamin yakin neman zabe

Kano - 'Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace duk wanda yayi zagon kasa garesa a Kano a zaben shugaban kasa da ke zuwa zai yi nadama, Daily Trust ta rahoto.

ganduje a baya-bayan nan ya sanar da magoya bayansa da ke jihar cewa, Kano za ta maimaita abinda ya faru a zaben shugaban kasa na 1993 lokacin da suka goyi bayan 'dan takarar kudu (marigayi MKO Abiola) tare da yin watsi da na jiharsu (marigayi Bashir Tofa), a kokarinsa na cewa za a zabi Tinubu a bar Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Kafa Sharadi 1 Da Zai Sa Ya Yi Wa Inyamurai Aiki Idan Zama Shugaban Kasa a 2023

Rabiu Musa Kwankwaso
Saura Kwanaki Kadan Zabe, Kwankwaso Ya Aike da Jan Kunne da Kakkausar Murya ga Ganduje. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Amma a yayin martani bayan kwanaki, Kwankwaso yace:

"Babu dadewa na yi rali wanda ya kasance mafi kyau. Na yi daya a Wudil, kudancin jihar, na yi daya a Bichi, arewacin jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Na bude ofishina a Kano ta tsakiya kuma rali mafi kyau da nayi mafi kyau saboda ba a gwada shi da irin na wasu 'yan takara da suka tara taron jama'ar da suka zo daga wajen jihar."
"Yanzu ka gani, ba na son batun wannan mutumin. Ban san ko yace ko bai ce ba, amma batun gaskiya shi ne, duk wanda yayi zagon kasa ga NNPP ko Kwankwaso a 2023, wata rana zai yi nadama kan kuskuren da ya tafka.
"Duk wanda ya san ni, ya san abinda na yarda da shi, idan na ci zaben shugaban kasa, Kano za ta fi ko ina mora, arewacin Najeriya da kasar baki daya.

Kara karanta wannan

2023: Ana Jiran G5 Ta Yanke Hukunci, Shugaban 'Yan Arewa Ya Tsoma Baki a Rikicin Wike da Atiku

'Toh ina mamaki idan ka je kana cewa in yi rali, rali dai na yi su da yawa a Kano. A cikin watannin Janairu da Disamna a Kano, na je yankuna uku na jihar, toh mene ne matsalar ka da yin rali na a Kano?"

- Kwankwaso yace.

Tsofafin zakarun Super Eagles sun je Kano yi wa Tinubu Kamfen

A wani labari na daban, tsofaffin zakarun Super Eagles sun dira jihar Kano domin taya Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugaban kasar Najeriya a jam'iyyar APC yakin neman zaben sa a 2023.

Shugaban KAROTA, Baffa Babba 'Dan Agundi ne ya karbesu tare da basu masauki a cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel