Zaben 2023: Buhari Ya Yi Gargadi Mai Tsauri Ga Kasashen Waje, Ya Gabatar Da Sabuwar Bukata

Zaben 2023: Buhari Ya Yi Gargadi Mai Tsauri Ga Kasashen Waje, Ya Gabatar Da Sabuwar Bukata

  • Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya ya yi kira ga jakadun kasashen waje kada su yi katsalandan a zaben 2023
  • Shuagban na Najeriya ya yi wannan gargadin ne yayin da ya ke bada wasikun kama aiki ga sabbin jakadun wasu kasashe ciki da Sudan ta Kudu, Ireland, Sweden da wasu
  • Buhari ya umurci su gudanar da ayyukansu bisa ka'ida da doka sannan ya nemi hadin kan kasashen don magance kallubalen da ke gaban Najeriya

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jakadun kasashen waje da aka turo Najeriya gabanin zabe su yi aikinsu bisa ka'ida da kwarewa, rahoton The Cable.

Femi Adesina, kakakin shugaban kasa, ya ce Buhari ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis yayin da ya ke mika wasikar kama aiki ga jakadun Switzerland, Sweden, Jamhuriyar Ireland, Thailand, Senegal, da Sudan ta Kudu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun koli ta yanke hukuncin karshe kan karar Mohammad Sani Abacha

Buhari
Buhari Ya Gargadi Kasashen Waje Kan Yi Wa Najeriya Katsalandan A Zaben 2023. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ku guji yin katsalandan a zaben Najeriya, Buhari ga sabbin jakadun kasashen waje

Buhari ya bukaci jakadun kada su yi katsalandan a zaben kasar kuma su mayar da hankalinsu kan aikin da aka turo su yi a kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari ya ce:

"Ina shawartar ku da kuyi aiki bisa tsarin jakadu kada ku wuce ka'ida a yayin da kuke sanya ido kan shirin zaben da babban zaben.
"Ina muku fatan nasara a dukkan ayyukanku sannan ina fatan za ku ji dadin yanayi da al'adun kasar mu yayin tafiye-tafiyen ku."

Shugaban kasar ya cigaba da cewa:

"Ina kyautata zaton an nada ku ne domin cigaba da nasarorin da magabatanku suka samu don bunkasa dangantakar mu zuwa mataki na gaba.
"A yayin da kuke fara ayyukan ku na jakadanci, ina fatan za ku yi la'akari da banbancin siyasa, rayuwa da tattalin arziki da al'adun kasar, wadanda sune abin alfaharin Najeriya."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya Ja Kunnen Ganduje Kan yi Masa Zagon Kasa a Zaben 2023, Yace Zai Tafka Nadama

Shugaban kasar ya nemi hadin kai daga kasashen domin magance kallubalen da ke fuskantar Najeriya.

Atiku: Buhari ya bani tabbacin za a yi sahihin zabe

Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023 ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar masa za a yi sahihin zabe a 2023.

Wazirin na Adamawa ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da Financial Times na Birtaniya, yana mai cewa sau biyu ga gana da Buhari kan batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164