Rikicin Ma'aurata
An sha yar dirama a wata kotu da ke yankin Dei Dei Abuja lokacin da wata matar aure da ta nemi a raba aurensu da mijinta tace ta fasa. Ta ce har yanzu tana sonsa.
Wani magidanci ya shiga hannun jami'an tsaro bayan ya yi yunkurin halaka matarsa har lahira. Jami'an yan sanda sun tabbatar da cafke shi a jihar Bauchi.
Wani dan Najeriya ya shiga hannun yan sanda a kasar Burtaniya bayan ya salwantar da ran matarsa wacce suka kwashe shekara 17 suna rayuwar aure tare.
Auren da ke tsakanin gwamnan jihar Yobe da diyar marigayi Sani Abacha ya zo karshe. Gumsu Sani Abacha ta tabbatar da mutuwar auren na ta da gwamnan.
Wani magidanci ya shigar da matarsa aure a gaban kotun shari'ar musulunci da ke Kano bisa zarginta da yin aure bisa aure. Ya nemu kotu ta raba auren.
Wata matar aure uwar yara uku, Rashidat Bashir, ta nemi Kotu a Ilorin ta raba aurenta saboda mijinta ya daina ɗaukar nauyinta da yayansu ga yawan zargi.
Wata amarya ƴar shekara 20 a jihar Adamawa ta ɗauki wani mummunan mataki kam angonta a jihar Adamawa. Amaryar ta cinnawa gidansa wuta saboda ya ƙi sakinta.
Wani miji ya bai wa matarsa hakuri da tsinken tsire guda biyu bayan sun samu sabani, bidiyon da ya yadu ya nuna yadda matar ta yafewa mijin bayan ya isa gareta.
Wata yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya kan wata hira mai daidaita zuciya da ta gano a wayar mijinta. Ta ce yanzu ji take kamar ita ke auren kanta.
Rikicin Ma'aurata
Samu kari