Zaben Ondo
Kasar Amurka ta ja hankalin Najeriya zuwa ga tabbatar da gudanarwar zaben gwamnan jihar Ondo wanda za a yi a ranar Asabar din nan cikin gaskiya da zaman lafiya.
Gabannin zaben gwamnan jihar Ondo, mambobin jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a birnin Akure.
Abdulsalami Abubakar, ya yi kira ga yan siyasa da su tabbatar da zaman lafiya da zabe na gaskiya a jihar Ondo gabannin zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar.
A yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamnan Ondo wanda za a yi a ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, an samu hargitsi a tsakanin yan bangar siyasa a birnin Akure.
Jagoran adawa Rabiu Musa Kwankwaso ya tara dinbin Hausawa, ya yi wa PDP baran kuri’u a Ondo. Babban ‘Dan siyasar ya yi kira ga ‘Yan Arewa da ke Ore su zabi PDP.
Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party ta yi korafi a kan yawan rikice-rikice da ake ta samu yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Ondo.
Gwamnatin APC za ta shimfida gadar da za ta hada Jihohin Ondo da Legas. Ana shirin hada Ondo da Legas ta doguwar gada domin rage yawan cinkoso a hanyoyin Legas.
Wata kotun majistare da ke zama a garin Akure, babban birnin jihar Ondo, ta bukaci da a adana mata wasu mutum 7 da ake zargi da zama 'yan daban siyasa daga Ifon
Gabannin zaben gwamnan jihar Ondo, sabon rigima ya kaure tsakanin jam’iyyun APC da PDP bayan an kama wasu yan daba dauke da makamai iri iri a cikin motar kamfe.
Zaben Ondo
Samu kari