Labaran tattalin arzikin Najeriya
Dan majalisar mazabar Damboa/Gwoza/Chibok a majalisar wakilai, Hon. Ahmadu Jaha ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya janye kudurin gyaran haraji daga majalisa.
Wasu daga cikin 'yan majalisar Arewa sun hade kai wajen adawa da kudirin haraji. Daga cikinsu har da 'yan jam'iyya mai mulki ta APC, inda ake neman sake duba batun.
Fadar Shugaban Kasa ta ce gyaran haraji ba zai fifita Lagos ya lalata Arewa ba kuma hukumomin NASENI, TETFUND da NITDA za su ci gaba da aiki kamar yadda aka saba.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa shi da takwarorinsa na jihohi sun bukatar a janye kudirin haraji ne domin a dawo a masu karin bayani.
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya gabatar da kasafin N382.5bn ga majalisar dokokin jiha, yana mayar da hankali kan cigaban tattalin arziki da jin dadin al'umma.
Gwamnatin tarayya ta fara cire harajin N50 kan kowace mu'amalar kudi ta N10,000. Kamfanonin Opay da Moniepoint sun fara aiwatarwa daga 1 ga Disamba.
Gwamnatin Legas ta tabbatar cewa ba ta da shirin haramta ruwan leda, tana mai da hankali kan magance sharar roba. Gwamnati ta gano masu kwacen ruwan leda.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ba Majalisar Tarayya shawarwari kan kudirin haraji inda ya ce ya kamata a sake duba abubuwan da ke ciki.
Majalisar Matasan Arewa ta caccaki Sanata Barau Jibrin da ya jagoranci zaman Majalisar kan sabon kudirin haraji inda ta ce kwata-kwata bai kishin yankin Arewa.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari