Abubuwa 5 da CBN Ya Kuskure Yayin Gabatar da Sabbin Takardun Naira, in Ji Wani Kwararre

Abubuwa 5 da CBN Ya Kuskure Yayin Gabatar da Sabbin Takardun Naira, in Ji Wani Kwararre

  • Sauya fasalin Naira da CBN ta yi ya samu martani da cece-kuce mai yawa a makwannin da suka gabata a Najeriya
  • Ka’idar sabbin kudi a Najeriya ta jawo zanga-zanga mai dumi, inda jama’a suka dinga koka rashin samun takardun kudi
  • Saboda haka ne wani kwararren masain tattalin arziki ya bayyana sharhinsa, inda ya fadi kadan daga inda CBN ya kuskure

Shirin babban bankin Najeriya (CBN) na sauya wasu daga kudaden Najeriya tare da rage amfani da tsabar kudi ya jawo cece-kuce a Najeriya.

Wani masani ya bayyana kadan daga inda babban bankin ya kuskure don samar da abin da yake bukata a wannan yanayi na rikicin tattalin arziki.

Taiwo Oyedele, kwararren kan harkar dokokin kudi kuma shugaban haraji a Afrika a PriceWaterCooper ya bayyana abubuwan da aka kaucewa daga bangaren CBN.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Yi Watsi da Buhari da CBN, Ya Tsawaita Wa'adin Amfani da Tsohon Naira a Jiharsa

Abubuwan da aka kuskure a lamarin sauya fasalin kudi
Kura-kuran CBN 5 a batun sauya fasalin kudi | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Da yake bayyana ra’ayinsa a Twitter a ranar 11 ga watan Faburairu, Oyedeke ya ce, ka’idojin CBN sun ma gaza cika ne tun daga yadda aka dauka batun sake fasalin Naira.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ga kadan daga inda CBN ya kuskure a wannan lamari na sauyi:

1. Tasirinsa ga tattalin arzikin kasa

A cewarsa, ya kamata hukumomin da ke da alaka da kudi a Najeriya su yi duba ga tasirin da sauyin fasalin kudin da ma rage amfani da tsabar kudi zai kawo.

Wannan ya hada da duba ga tasirin hakan ta fuskar hauhawar farashi, habakar tattalin arziki, aikin yi da kuma gwargwadon kashe kudin gama-garin mutane.

2. Batun tsaro

CBN da sauran hukumomin kudi ya kamata su duba lamarin da ya shafi tsaro wajen sauya fasalin Naira da kuma kawo dokar rage kashe tsabar kudi.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Yadda Gwamnan CBN Zai Jefa Kan Shi a Cikin Matsala – Shugaban PACAC

Wannan ya hada da nemo hanyar yakar buga kudaden bogi, damfara da dai sauran manyan laifukan da ke da alaka da barna ta kudi.

3. Yadda jama’a za su iya samun damar samun kudin

Hakazalika, ya kamata hukumomin su yi duba ga yadda ayyukan musayar kudi za su kasance kafin sauya Naira da kawo dokar rage kashe tsabar kudi.

Kadan daga abubuwan lura a nan su ne; duba ga masu karamin karfi da kuma wadanda ke neman halaliyarsu ta kananan sana’o'i, har da duba ga wadanda basu da asusun banki da kuma wadanda basu iya ta’ammuli da hanyoyin musayar kudi na zamani ba.

4. Kudin da za a kashe wajen yin aiki

A cewarsa, ya kamata CBN ya duba tare da yin nazari kan kudaden da za a kashe wajen sauya fasalin kudi da kuma tabbatar da dokar rage kashe takardun kudi.

Daga cikin abin da ya kamata CBN din ya duba akwai kudin da za a kashe wajen buga kudin, hanyoyin samar da ababen musayar kudi da kuma kudin da za a kashe wajen wayar da kan mutane game da canjin da aka samu.

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

5. Ra’ayin jama’a

Ba wai kawai kawo dokar ba, a cewar Oyedele ya kamata CBN ya nemi shawarin ‘yan kasa da kuma jin martaninsu game da dokokinsa.

A cewarsa, kamata ya yi CBN ya yi duba ga abin da mutane za su da kuma irin tsaiko, cece-kuce da rudanin da sauyin kudin zai kawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel