Hukumar yan sandan NAjeriya
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Zamfara. Miyaguk sun yi awon gaba da mutane zuwa cikin daji tare da kashe wasu daban.
Wani dan sanda ya saki wuta a wurin bincike ababen hawa a jihar Benuwai, harsashi ya yi ajalin wata daliba da ke ajin karshe a jami'a ranar Juma'a.
Ya sanda a Jihar Rivers sun tabbatar da kama wata mata mai suna Gift bayan ta yanke mazakutar saurayinta a unguwar Diobu da ke Port Harcourt a jiya Alhamis.
An yi ta yada bidiyo dauke da matasa 89 da aka ce sun je Lagos daga Katsina domin yin aiki a matatar Aliko Dangote, yan sanda sun yi bincike da tabbatar da gaskiya.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun farmaki shingen bincike a yankin mahaifar mai girma gwamnan jihar Anambara, Farfesa Charles Soludo.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun sake kai harin ta'addanci a jihar Plateau. Miyagun sun hallaka mutane takwas a harin da suka kai a cikin dare.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace basarakena jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, ƴan sanda sun fara farautarsu domin ceto shi.
An samu barkewar rikicin manoma da makiyaya a wasu kauyukan jihar Taraba. Rikcin ya jawo an samu asarar rayukan mutane daga bangaren manoma da makiyaya.
Gwamnan jihar Zamfara ya tabo batun matsalar rashin tsaron sa ake fama da ita. Ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta hawa teburin sulhu da 'yan bindiga.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari