Jihar Niger
Rundunar sojojin saman Najeriya ta kai hare-hare kan maboyar 'yan ta'addan da suka addabi mutane a jihar Neja. An hallaka tsagerun tare da lalata maboyarsu.
Miyagun 'yan bindiga sun hari a wasu kauyukan jihar Neja inda suka kwashe kayan abinci da sauran kayayyaki masu amfani. Mutanen kauyukan sun tsere.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yauzu haka ta na tunanin sauyawa daurarrun da ke Suleja matsuguni domin dakile yunkurinsu na guduwa daga fursun din
Mazauna kauyen Allawa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja sun shiga fargaba bayan sojoji sun tattare kayansu a kauyen sun fice da safiyar yau Alhamis.
Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCOs) ta tabbatar da cewa ta cafko wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan gyaran hali a Neja.
Rahotanni sun nuna cewa fursunoni da dama sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja bayan da ruwan sama ya lalata katangar ginin gidan yarin.
Akalla sojoji shida ne aka kashe a kauyen Karaga da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja bayan sun fada wani tarko da 'yan bindiga suka dana masu.
Wasu 'yan bindiga sun hallaka akalla sojoji shida a jihar Neja tare da yin garkuwa da wani Kyaftin a wani mummunan hari a daren Juma'a 19 ga watan Afrilu.
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya bawa jami'an tsaro umarnin harbe 'yan daba nan take tare da sanya dokar ta baci a jihar. Dokar ta biyo bayan wani hari ne a jihar
Jihar Niger
Samu kari