Musulmai
Wasu majiyoyi sun tabbatar mana da cewa Allah ya karbi rayuwar fitaccen malamin Musulunci a jihar Bauchi, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi bayan fama da jinya.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa ya yi bayani kan hukunce hukunce azumin sittu Shawwal. Malamin ya ce sittu Shawwal Sunnah ne kuma ana son fara rama Ramadan kafin shi.
Sanata Magatakarda Wamakko ya kafa kwamiti bayan wani mutum mai suna Musa Abubakar ya yi ridda saboda tsoron ’yan bindiga, ya sake karɓar addinin Musulunci.
Shugabannin musulmi da ke zaune a jihar Ribas sun bukaci shugaban kasa Ɓola Ahmed Tinubu ya sake nazari kan doka ta ɓaci kuma ya maida dakataccen Gwamna Fubara.
Bayan zarge-zargen Ɗan Bello kan Sheikh Bala Lau, Malam Alkali Abubakar Salihu Zaria ya gargadi matashin kan kalamansa inda ce dole za su dauki mataki.
Baban Chinedu ya bayyana cewa ya fara fuskantar barazana tun daya fara wa'azin kare addinin Musulunci. Baban Chinedu ya ce a yanzu haka ba ya iya kwana a gida.
Wata ƙungiyar musulmi (TMC) ta buƙaci al'umma su kwantar da hankulansu, ka da a ɗauki fansa kan kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa mafarauta a Edo.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gwangwanje mutanen da ke ɗaure a gidajen gyaran hali da tallafin kayan abinci da shanu 12 sabida su yi shagalin sallah.
Bayan kammala sallar idi a Gombe, rahotanni sun tabbatar da cewa an samu turmutsutsu yayin da yara biyu suka rasa rayukansu sannan wasu 20 suka jikkata.
Musulmai
Samu kari