Hotunan wasu ƴan kabilar Igbo yayin da suke karɓar shahada a masallacin Jihar Enugu

Hotunan wasu ƴan kabilar Igbo yayin da suke karɓar shahada a masallacin Jihar Enugu

Jihar Enugu - Wasu mutane biyu yan kabilar Igbo, Chizoba da Chidera sun karbi addinin musulunci a Jihar Enugu.

A cewar wani Muhammad Kabir Orjiegbulam, sun karbi shahadar ne a babban masallacin Ibagwa-Aka, Igbo-Eze South Local Government a ranar Juma'a, 28 ga watan Janairu kamar yadda ya wallafa a dandalin sada zumunta.

Ya rubuta:

"Allahu Akbar. Sun karbi addinin musulunci yau a babban masallacin Ibagwa-aka a Jihar Enugu, Ɗan uwa Chizoba yanzu ya zama Musa, yar uwa Chidera kuma ta zama Adina. Allah ya sa su zama masu amfani ga musulunci a ƙasar Igbo. Amen."

Shima Bulama Muhd Bukar ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter.

Hotunan wasu ƴan Igbo da suka karɓi addinin musulunci a Jihar Enugu
Wata budurwa da saurayi yan kabilar igbo sun karbi musulunci a Enugu. Hoto: Muhammad Kabir Orjiegbulam
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Tinubu ganawa da wasu yaje yi Landan, ba jinya ba: Hadiminsa ya bayyana ranar da zai dawo

Hotunan wasu ƴan Igbo da suka karɓi addinin musulunci a Jihar Enugu
Wasu Igbo yayin karbar musulunci a masallaci a Enugu. Hoto: Muhammad Kabir Orjiegbulam
Asali: Facebook

Hotunan wasu ƴan Igbo da suka karɓi addinin musulunci a Jihar Enugu
Wasu 'yan kabilar Igbo sun karbi musulunci a Enugu. Hoto: Muhammad Kabir Orjiegbulam
Asali: Facebook

Martanin wasu mutane

@Suleiman24451914 ya ce:

"Masha Allah"

@OlayinkaOmole2 ya ce:

"Da fatan haka za mu yi idan musulmi ya koma kirista"

@TeyhilaVhayil ya ce:

"Duk wani igbo da ya bar kiristanci ya koma musulunci ba abin yarda bane.

Suna neman sauya rayuwa ne a kan abin da suke da shi. Ku bincika abin da aka musu alkawari"

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel