Masu Garkuwa Da Mutane
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan bindiga 11 a wani samame da suka kai jihar Zamfara da Katsina, kuma sun lalata sansanin 'yan bindiga.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa yayin samamen haɗin guiwa na sojoji an yi nasarar kashe ƴan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar Kuriga.
'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari cikin cocin Celestial da ke jihar Ogun inda suka sace mambobin cocin su na tsaka da gudanar da bauta a kauyen Oriyarin.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai sama da 100 na makarantar kauyen Kuriga da aka ceto daga hannun ƴan bindiga kwanan nan.
Asibitin kwararru na Reliance da ke Sokoto a ranar Laraba ya musanta cewa ya yi jinyar shugaban ‘yan bindiga Dogo Gide, wanda sojoji suka harbe shi.
Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi zaman sulhu da 'yan bindiga a yunkurinta na magance matsalar tsaro a Najeriya.
Wani shafin yanazar gizo mai tsage gaskiya ya tabbatar da cewa ikirarin cewa an yi awon gaba da mai ɗakin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ba gaskiya bane.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya koka kan yawaitar ayyukan masu garkuwa da mutane. Ya bayyana su a matsayin 'yan ta'adda wadanda za a kawo karshensu.
Wasu maharan sun yi garkuwa da matan aure 12 da namiji ɗaya, sun kwashi dukiyar bayin Allah mai ɗumbin yawa a karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari