Masu Garkuwa Da Mutane
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana hakikanin adadin yawan daƙiban da aka sace. Gwamnan ya ce adadin dalibai 137 da aka ceto shi ne na gaskiya.
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya karyata cewa Sheikh Ahmed Gumi ya taka rawa wurin kubutar da daliban makaranta a jihar Kaduna inda ya ce ko sisi ba a biya ba.
Hedikwatar tsaro ta kasa ta fitar da bayanai kan daliban da aka ceto daga hannun 'yan bindiga a jihar Kaduna. An dai ceto daliban ne a jihar Zamfara.
Yaran makarantar da aka sace a Kaduna tun a farkon wata sun fito. Uba Sani a jawabin da ya fitar a Facebook, ya yi wa Allah Sarki SWT godiyar nasarar da aka samu.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar dakile wani yunkuri da 'yan bindiga suka yi na yin garkuwa da mutane. Sun yi musayar wuta tare da fatattakarsu.
Rahotannin sun tabbatar da cewa daliban tsangaya 15 da aka sace su a jihar Sokoto sun kubuta daga hannun 'yan bindigan makwanni biyu bayan maharan sun dauke su.
Wani sabon ango mai suna Sani yana daga cikin mutane 21 da ‘yan bindiga suka kashe a wata kasuwar mako a garin Madaka, karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa magajin gari da wasu mutane 20 sun ru yayin da ƴan bindiga suka kai farmaki wani kauyen karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Radda tare da dakarun sojin saman Najeriya sun yi nasarar ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su a dajin Jibia.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari