Gwamnan Bauchi Ya Gina Katafaren Gida Yayin da Talaka Ke Shan Wuya a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana
- Wasu hotuna da suka yaɗu sun nuna wani sabon gida da ake zargin, Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, ya gina a asirce yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya
- Wannan iƙirarin ƙarya ne kamar yadda bincike ya nuna cewa hoton da ake magana a kai yana kan yanar gizo tun shekarar 2020
- Saɓanin jita-jitar, hoton ya nuna ƙofar shiga wani katafaren gida ne na wani fitaccen kamfanin gine-gine a jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Bauchi, jihar Bauchi - Wani hoto da ke yawo a yanar gizo ya yi iƙirarin cewa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya gina wani katafaren gida na sirri.
Mutane da dama sun yaɗa hoton a shafin shafin sada zumunta na Facebook, inda suka nuna hoton wani ƙaton gida wanda ake kan gininsa yanzu haka.
Sun bayyana cewa sabon gidan wani gwamna ne wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ɓangare na rubutun na cewa:
"Abin da yake tashe: Wannan ba filin jirgin sama ba ne ko otel. Ana zargin gidan gwamnan jihar Bauchi ne, mai girma Bala Mohammed, kuma ana kan gina shi.
"Haƙika, mugaye ne cikin fatar mutum ke jagorantar mu."
Ana kuma iya ganin irin wannan batu a nan da nan.
Har ila yau, labarin ya yi yawo a manhajar nan ta tura saƙonni watau WhatsApp.
Menene gaskiya kan batun?
Domin yawancin masu amfani da intanet sun yi amanna da batun, wani dandali na binciken gaskiya, Dubawa, ya yanke shawarar gano gaskiya kan lamarin.
Bayan bincikensa, Dubawa ya gano cewa hoton da aka yi amfani da shi don nuna gidan gwamnan yana kan yanar gizo tun 2020.
Kafar yaɗa labaran ta bayyana cewa an ɗauki hoton ne a lokacin da ake gina babbar ƙofar shiga wani katafaren gida da ke Simawa, mai tazarar kilomita kaɗan daga sansanin cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) a jihar Ogun.
Ginin mai suna 'Cape Town' mallakar Adron Homes and Properties ne, wani sanannen kamfani gine-gine a Najeriya.
Don haka maganar cewa Mohammed na gina katafaren gida a ɓoye ƙarya ce.
Gwamna Bala Ya Gana da Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya gana da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Gwamna Bala Mohammed ya sanya labule da tsohon gwamnan na jihar Rivers ne, saboda batun zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
Asali: Legit.ng