An Shiga Jimami Kan Rasuwar Shugaban Jam'iyyar PDP, Bayanai Sun Fito

An Shiga Jimami Kan Rasuwar Shugaban Jam'iyyar PDP, Bayanai Sun Fito

  • Jam'iyyar PDP a jihar Ondo ta yi babban rashi na shugabanta a jihar wanda ya yi bankwana da duniya a safiyar ranar Laraba
  • Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar PDP a jihar Ondo, Sunshine Kennedy Peretei, ya tabbatar da rasuwar Fatai Adams
  • Sai dai, sakataren bai bayar da cikakkun bayanai ba kan rasuwar shugaban jam'iyyar, inda ya ce nan ba da jimawa ba zai yi hakan a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Rahotanni sun bayyana cewa shugaban jam’iyyar PDP na jihar Ondo, Fatai Adams ya rasu.

Har yanzu dai ba a bayyana cikakken bayani kan rasuwarsa ba, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto.

Shugaban PDP na Ondo ya rasu
Fatai Adams ya rasu da sanyin safiyar ranar Laraba Hoto: Ondo PDP Vanguard
Asali: Twitter

Sai dai, rahotan jaridar The Nation ya bayyana cewa shugaban na PDP ya rasa ransa ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairun 2024.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya yi wa Tinubu wankin babban bargo, ya gargadi Abba Gida Gida kan abu 1 tak

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP a jihar, Sunshine Kennedy Peretei ya tabbatar wa manema labarai rasuwarsa.

Sakataren ya ƙara da cewa nan ba da jimawa za su yi magana da manema labarai a hukumance kan lamarin.

Peretei ya ce:

"Eh, gaskiya ne, amma nan ba da jimawa ba za mu yi magana da ku a hukumance kan lamarin."

An dakatar da Fatai Adams daga muƙaminsa

A kwanakin baya ne dai jam'iyyar PDP a jihar Ondo ta dakatar da Fatai Adams daga kan muƙaminsa bisa zarginsa da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.

Jami'iyyar ta kuma zargi Fatai wanda aka zaɓa a watan Agustan 2020 da laifin jawo wa jam’iyyar zubewar mutuncinta a idon duniya.

Dakatarwar da aka yi wa Fatai dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke shirye-shiryen tunkarar zaɓen gwamnan jihar a wannan shekarar ta 2024.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gama shiri, ta faɗi jiha 1 da zata ƙwace mulki daga hannun gwamnan PDP a 2024

PDP Ta Magantu Kan Dakatar da Fatai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar PDP (NWC) ya yi watsi da batun dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar Ondo, Fatai Adams.

Kwamitin na NWC ya yi fatali da dakatarwar wacce ya bayyana a matsayin ba ta inganta ba domin ba ta yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam'iyyar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel