Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Fadi Abu 1 da 'Yan Najeriya Ya Kamata Su Yi Wa Shugabanni

Tsadar Rayuwa: Sarkin Musulmi Ya Fadi Abu 1 da 'Yan Najeriya Ya Kamata Su Yi Wa Shugabanni

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira ga ƴan Najeriya da duk tsanani su riƙa mutunta shugabanninsu
  • Sarkin Musulmin ya yi nuni da cewa kamata ya yi a riƙa komawa wajen Allah domin neman sauƙi duk lokacin da abubuwa suka rincaɓe
  • Ya buƙaci ƴan Najeriya da su riƙa sanya shugabanni ciki addu'o'insu domin samun magance ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Iseyin, jihar Oyo - Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su yi watsi da shugabanninsu, sai dai a yi musu addu'a, don samun nasara a cikin aiki mai wahala na sake fasalin ƙasar nan.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da babban masallacin Iseyin da aka gyara, Sarkin Musulmin ya ce duk tsanani dole ne a mutunta shugabanni domin Allah ne ya sanya su, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

Sarkin musulmi ya shawarci 'yan Najeriya
Sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su mutunta shugabanni Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Twitter

A cewarsa, Allah ne ya yi shugabanni kuma shi kaɗai ya kamata a nemi sauƙi daga wajensa idan mutane suka gamu da wahalhalun da ba a san su ba ta hanyar gudanar da mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kammala jawabin nasa inda ya amince da jawabin da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi game da halin da al’ummar ƙasa ke ciki na yunwa da fushi.

Sai dai, ya buƙaci ƴan Najeriya su riƙa yi wa shugabanninsu addu’a maimakon su riƙa faɗin munanan kalamai a kansu komai tsanani.

A kalamansa:

"Allah ne ya yi shugabanni kuma shi kaɗai ya kamata a nemi sauƙi daga wajensa idan mutane suka gamu da wahalhalun da ba a san su ba ta hanyar gudanar da mulki.
“Na saurari gwamna, (Seyi Makinde) kuma yana magana cike da tausayi. Haka ya kamata shugaba ya yi magana da jama'arsa. Su sani ka damu da su domin Allah Ta’ala zai tambaye ka me ka yi musu."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Babban malamin addini ya tura sako mai muhimmanci ga Shugaba Tinubu

Malamin Addini Ya Yi Muhimmin Kira Ga Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu shawara daga wajen babban limamin cocin Anglican ta Ikwerre a jihar Rivers.

Fasto Blessing Enyindah ya shawarci shugaban ƙasan da ya gaggauta tsamo ƴan Najeriya daga halin ƙuncin da suka tsinci kansu a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel