Manyan Labarai A Yau
Daniel Bwala wanda a baya ya rike mukamin kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa, ya ce bai yi nadamar goyon Atiku da jam'iyyar PDP ba a zabeɓ 2023.
Bangaren siyasa na kungiyar NLC ya bukaci shugaban jam'iyyar Labour Party na kasa (LP), Julius Abure, da ya yi murabus daga mukaminsa na shugabancin jam'iyyar.
Wasu gungun miyagun 'yan ta'adda dauke da makamai sun sake kai harin ta'addanci a wani kauye da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, a ranar Asabar.
Gwamnatin jihar Kogi ta fito ta kare tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, kan zargin karkatar da N100bn da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ke yi masa.
Sanannen malamin addinin musuluncin can, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ya fadi kuskuren da gwamnatin tarayya ke yi wajen kawo karshen 'yan bindiga.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaro Bago, ya bada hutun kwanaki biyar a jihar domin raba kayan tallafi a fadin jihar. Hutun zai fara mako mai zuwa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi sabo nadi a hukumar yaki da yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA). Shugaban kasan ya ba Dakta Temitope shugabancin hukumar.
'Yan bindigan da suka yi garkuwa da dalibai a jihar Kaduna, sun aika da bujayarsunkan kudaden fansan da za a biya kafin yaran su shaki iskar 'yanci.
Sanata Abdul Ningi wanda majalisar dattawa ta dakatar kan zargin yin cushen N3.7tr a kasafin kudin shekarar 2024, ya yi zargin cewa ana shirin cafke shi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari