Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin wani babban nadi da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi. Ya nada sabon shugaban hukumar NIMASA.
Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kungiyar Sanatocin Arewa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya labule da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, bayan majalisar ta dakatar da Sanata Abdul Ningi.
Majalisar dattawa ta dauki matakin kan Sanata Abdul Ningi wanda ya yi zargim cewa an yi cushe a kasafin kudin shekarar 2024. An dakatar da shi na wata uku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a babban zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi martani kan jita-jitar cewa yana shirin sauya sheka daga jam'iyyar.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci gwamnonin jihohin kasar nan da su samar da filayen kiwo ga makiyaya don kawo karshen rikicinsu da manoma.
Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya dauki matakai masu tsauri wadanda suka dace don kawo karshen 'yan ta'adda.
An yi kazamin karo tsakanin mutanen kauyen Tswako Makun da na Gbangba Dzuko, a karamar hukumar Gbako ta jihar Neja. Lamarin ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi.
Fadar shugaban kasa Bola Tinubu ta bayyana cewa Godwin Emefiele ya cire biliyoyin daloli a asusun kasar ba tare da sanin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari