Rigima Sabuwa: An Bukaci Shugaban NLC Ya Yi Murabus, An Fadi Dalili

Rigima Sabuwa: An Bukaci Shugaban NLC Ya Yi Murabus, An Fadi Dalili

  • Babban taron da jam’iyyar Labour Party (LP) ke shirin yi a birnin Umuahia na jihar Abia ya haifar da sabon faɗa tsakanin jam’iyyar da ƙungiyar NLC
  • Rikicin ya ɓarke ne tsakanin Julius Abure da Joe Ajaero yayin da NLC ta ƙalubalanci babban taron da jam'iyyar ke shirin yi
  • A nasa jawabin, Abure ya buƙaci Ajaero da ya yi murabus ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar LP idan da gaske yana da son karɓar muƙamin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Shugaban jam’iyyar Labour Party (LP) ya buƙaci shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero da ya yi murabus ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar.

Jam’iyyar adawar ta yi wannan kiran ne a lokacin da take mayar da martani ga wata wasiƙa da ɓangaren siyasa na NLC ya rubuta, inda ya buƙaci a dakatar da babban taron jam’iyyar LP da za a yi a Umuahia, jihar Abia, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Rayuwa ba tabbas: Direba ya fadi ya rasu yana tsaka da tuka dalibai zuwa makaranta

Jam'iyyar Lp ta caccaki Ajaero
Jam'iyyar LP ta bukaci Ajaeto ya yi murabus daga shugabancin NLC Hoto: Nigeria Labour Congress HQ, Labour Party TV
Asali: Facebook

Legit Hausa ta kawo rahoto cewa, ɓangaren siyasa na NLC ya bukaci shugaban jam'iyyar na ƙasa, Julius Abure da ya gaggauta yin murabus tare da kafa kwamitin riƙon ƙwarya da zai jagoranci gudanar da babban taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa a ranar Asabar, 16 ga watan Maris, ta hannun sakataren yaɗa labaranta na kasa, Obiora Ifoh, jam'iyyar LP ta dage cewa taron da aka tsara zai gudana kamar yadda aka tsara, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.

Me jam'iyyar LP ta ce kan Ajaero?

Jam’iyyar ta ce shiga hanci da ƙudundunen da shugaban NLC, Ajaero, ke yi mata ya lalata nasarorin da ta samu.

Jam’iyyar ta ce katsalandan ɗin da ƙungiyar ta NLC ke yi a al’amuranta ya zama abin damuwa, kuma ya kamata a sanar da NLC cewa LP na da irin na ta salom wanda ya sha bamban da na ƙungiyar.

Kara karanta wannan

Na hannun daman Atiku ya fadi nadamar da ya yi kan aiki da tsohon mataimakin shugaban kasan

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Shugabannin jam'iyyar sun yanke shawarar kiran babban taron na ƙasa.
"A wannan gaɓar, shugabannin jam'iyyar na son tambayar NLC, wai takamaimai me suke so? Idan Joe Ajaero yana son shugabancin jam'iyyar, ana shawartarsa da ya yi murabus daga shugabancin NLC ya zo ya nemi takarar shugabancin jam'iyyar a zaɓen da za a gudanar lokacin babban taro na ranar 27 ga watan Maris, 2024.

Shugabancin LP: Kotu ta tabbatar da Abure

A wani labarin kuma, kuma kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na ƙasa.

Kotun ta soke hukuncin da wata babbar kotu ta yi a baya na haramtawa Abure bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel