Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar, da kuma hanyoyin da za a bi domin kawo karshenta.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta ki amincewa da bukatar neman beli da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya gabatar.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Akwa Ibom. Miyaguk dauke da makamai sun shiga har cikin coci sun hallaka wanda ya kafa ta tare da babban fasto.
Fusatattun dakarun sojoji sun kai farmaki kan maboyar shugaban 'yan ta'addan da ke da hannu a kisan da aka yi wa sojoji 16 a jihar Bayelsa. Sun kona gidaje.
Wani dan kunar bakin wake ya salwantar da ransa bayan ya tayar da ban din da ke tattare da shi a jihar Borno. Wasu mutum biyu sun jikkata sakamakon tada bam din
Wani jigo a jam'iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju, ya yi magana kan umurnin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar na aiwatar da rahoton Steve Oronsaye.
Wasu miyagun 'yan ta'adda da ke dauke da makamai sun kai sabon harin ta'addanci cikin dare a jihar Kaduna. 'Yan ta'addan sun yi awon gaba da mutum 87.
Jami'an tsaro na 'yan sa kai, sun samu nasarar tura kasurgumin shugaban 'yan bindigan, da ya dade yana addabar mutane a jihar Katsina zuwa lahira.
Majalisar dattawa ta yi martani kan kisan gillar da aka yi wa jami'an sojoji 16 a jihar Delta. Majalisar ta bukaci a tabbatar da cewa maharan sun fuskanci hukunci.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari