An Fadi Abin da Ya Kamata Tinubu Ya Fara Yi Kafin Aiwatar da Rahoton Oronsaye

An Fadi Abin da Ya Kamata Tinubu Ya Fara Yi Kafin Aiwatar da Rahoton Oronsaye

  • An buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ƙara kaimi wajen aiwatar da alƙawurran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe
  • Rilwan Olanrewaju, jigo a jam’iyyar PDP, a wata hira da Legit.ng, ya bayar da misali da yawan ministocin Tinubu, a matsayin saɓanin alƙawarin da ya yi na rage kashe kuɗi a gwamnati
  • Da yake magana kan matakin da shugaban ƙasan ya ɗauka na aiwatar da rahoton Oronsaye, jigon na PDP ya yi mamakin dalilin da ya sa Tinubu ya naɗa ministoci masu yawa bayan ya san yana son tsuke bakin aljihun gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya mayar da hankali wajen rage kashe kuɗi a gwamnati, maimakon faɗi a baki kawai.

Kara karanta wannan

Rayuwa ba tabbas: Direba ya fadi ya rasu yana tsaka da tuka dalibai zuwa makaranta

Wannan kiran na zuwa ne bayan shugaban ƙasan ya bayar da umarnin a aiwatar da rahoton Steve Oronsaye.

Jigo a PDP ya caccaki Tinubu
A lokacin yakin neman zabe Tinubu ya yi alkawarin tsuke bakin aljihun gwamnati Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Da yake martani kan umarnin, Rilwan Olanrewaju, wani jigo a jam'iyyar PDP, a yayin wata tattaunawa da Legit.ng, ya ce shugaban ƙasan surutu kawai yake yi wanda har yanzu ba a gani a aikace ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ba gaskiya a gwamnatin Tinubu' - Rilwan

Olanrewaju ya yi nuni da yawan ministoci da masu bada shawara na musamman na Tinubu, sun fi waɗanda aka samu a ƙasar nan a lokacin mulkin magabatansa.

A kalamansa:

"Tuntuni ya kamata a aiwatar da rahoton Oronsaye, amma tambayar ita ce ko za a iya aiwatar da shi gaba ɗaya. Ɗaya daga cikin matsalar da na ke da ita da gwamnatin APC ita ce rashin gaskiyarsu.

Kara karanta wannan

Sace-sace a Kaduna da Borno: An ba Shugaba Tinubu mafita

"Tsuke bakin aljihun gwamnati shi ne mafita, sannan dole ya fara daga kan shugaban ƙasa. Yi tunani a kai, shugaban ƙasan da ya amince da rahoton kuma ya ƙirƙiro ƙarin ma'aikatu domin ya sanya na kusa da shi.
"Ka da ka manta muna samun ministoci 43 - 45, amma yanzu muna da minsitoci 48. Mun ji cewa yana son rage yawan hukumomi, ban ga wata gaskiya ba a ƙoƙarinsa na tsuke bakin aljihun gwamnati.
"Abu na biyu, wanda yake son aiwatar da rahoton, ba zai tara hadimai daban-daban kan aiki iri ɗaya ba, idan ka duba hadimansa, za ka ga cewa mutum huɗu na yin aiki iri ɗaya inda ake biyansu maƙudan kuɗi."

Rahoton Oronsaye: Makomar ma'aikatan gwamnati

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana makomar ma'aikatan gwamnati saboda aiwatar da rahoton kwamitin Steve Oronsaye.

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Mohammeɗ Idris, ya bayyana cewa mutane ba za su rasa aikinsu ba saboda kwaskwarimar da za a yi wa ma'aikatun gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng