Labaran Soyayya
Wani dan Najeriya ya garzaya dandalin TikTok don shawartan mazajen da ke tafiya turai suna barin matayensu a gida. Bidiyon ya haddasa cece-kuce daga jama’a.
Wani mai hoto a Najeriya ya yi fushi da kanwar amarya da ta hana shi abinci a wajen bikin, don haka ya hukunta budurwar ta hanyar yanketa a gaba daya hotunan.
Wani ango da amaryarsa sun samu gudunmawar galan babu komai ciki a wajen bikinsu. An dauki bidiyon wannan lamari mai ban mamaki kuma ya yadu a dandalin TikTok.
Wata budurwa ta rabu da matashin da ya buɗe mata shago domim fara sana'a, amma sai ta rabu da shi bayan arziƙinsa ya yi ƙasa ta koma soyayya da kwastomanta.
Wani mashahurin dan damfara ya dauko hayar sojoji don kama wani malamin Musulunci mai suna Sulaimon saboda addu'ar bogi da ya masa bai ci nasara ba a aikinsa.
A garn Benin, da wani matashi ya ji labari sahibarsa za ta yi aure, sai Osayande Efosa ya aika hoton batsa ga wanda yake neman ta da niyyar lalata maganar.
Wata baturiya ta garzaya soshiyal midiya don fallasa wani masoyinta dan Najeriya wanda ya barta tana da cikin mako 39 a Turai sannan ya auri wata a Najeriya.
An fasa auren wata tsohuwar dalibar jami’ar jihar Abia mai shekaru 30 bayan aminin angon ya fallasa irin mummunan rayuwar da ta yi a lokacin da take makaranta.
Wani matashi ya nuna hirar da suka yi da tsohuwar budurwarsa wacce suka rabu. Budurwar ta yi magana bayan ta ga ya siyo sabuwar mota inda ta nemi su sasanta.
Labaran Soyayya
Samu kari