Labarin Sojojin Najeriya
Hafsun tsaron Najeria, Janar Cristopher Musa ya ce 'yan siyasa na da hannu a karuwar rashin tsaro a Najeriya. Ya ce zaben 2027 na da alakada karuwar hare hare.
Janar Christopher Musa ya ce ‘yan ta’adda sun koma amfani da zinare wajen daukar nauyin ayyukan ta'addanci, sannan ya shawarci ‘yan Najeriya da su koyi dabarun faɗa.
Dakarun soji sun kama wata jaka cike da harsashi ana shirin tafiya da shi jihohin Arewa ta Yamma da ke fama da matsalar 'yan bindiga. Motar ta fito daga Borno.
An samu nasarar cafke wasu yan ta'adda bayan hukumar tsaro ta Najeriya ta taimakawa kasar Chadi wurin tabbatar da kama dan wanda ya kafa Boko Haram, Mohammed Yusuf.
Rahotanni daga jihar Borno sun tabbatar da tashin wani bam da yara yan gwangwan suka dauko a bayan gari, mutum biyu sun jikkata yayin wasu 4 suka raunata.
Sojin saman Najeriya sun kai farmaki a sansanin 'yan bindiga da ke Danmusa, jihar Katsina, sun kubutar da mutum 62, gwamna Radda ya yaba da jarumtar jami’an tsaro.
Yaran dan ta'adda, Bello Turji sun kai hare hare jihar Sokoto. Sun kashe mutane da dama tare da sace wasu. Sojoji sujn ce har yanzu suna neman Turji ido rufe.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya sanar da cewa jami'an tsaro sun samu nasarar cafke shugaban kungiyar 'yan ta'addan, Ansaru.
Rahotanni daga rundunar sojin Najeriya sun nuna cewa an samu wata fashewa a dakin ajiya da je Barikin Ilese a jihar Ogun amma babu wanda ya rasa ransa.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari