Labarin Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya sun tarwatsa bikin 'yan bindiga da ruwan bama bamai yayin da suke tsaka da bikin aure a dajin Zamfara. An kashe 'yan ta'adda da dama a farmakin.
A labarin nan, za a ji cewa mazauna Zamfara sun shiga tashin hankali bayan wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da basarake jim kaɗan bayan korarsu daga yankin.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani mummunan harin 'yan bindiga a jihar Zamfara. Sojojin sun kuma kwato makamai daga hannun tsagerun.
Dakarun sojin Najeriya sun kama wani matashi a jihar Borno dauke da man fetur, sirinji, wasu kayayyakin tsari da ake zargi zai mika su ga Boko Haram ne.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas, sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Boko Haram yayin wani artabu.
Ana zargin yaran Bello Turji sun kai hari a wani yanki na Shinkafi a jihar Sokoto. Sun kashe wani matafiyi Yusuf Isah kafin dakarun soji Najeriya su fatattake su.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a jihohin Borno da Adamawa.
Wasu tsofaffin sojoji sun mamaye hedikwatar ma’aikatar kudi a Abuja, suna neman a biyan alawus, giratuti da albashin da aka rike tun bayan barin aiki.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da matan da suka shiga cikin daji neman itace. Jami'an tsaro sun fara kokarin ganin sun kubutar da su.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari