Labaran garkuwa da mutane
Mun kawo wuraren ‘Yan ta’adda ke shirin kai wa hari a birnin tarayya. ‘Yan ta’addan Boko Haram da ‘Yan bindiga sun tare a wasu unguwanni a Birnin na Abuja.
Bayan ya kubuta kuma ya haɗu da iyalansa, ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya ce yana tausaya wa ragowar da ke hannun yan ta'adda.
Za a ji shugaban jam’iyyar NNPP a Katsina ya yi kira ga Mai girma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ajiye mulki, Jam’iyyar NNPP ta koka kan batun tsaro.
A wata hira da aka yi dashi, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano ya bayyana irin takaicin da yake ji game da alakar 'yan ta'adda da wasu alkalai a Najeriya.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, saboda fargabar fargabar hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, ta bayar da umarnin rufe dukkanin kwalejojin gwamnatin tarayya.
'Yan ta'adda sun sako mutane uku cikin fasinjojin 62 da suka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris din wannan shekarar.
A daren yau aka dauke Sunday Odoma Ojarum da Janet Odoma Ojarume. ‘Yan bindiga sun kutsa har gidan na su, suka dauke su a lokacin da al’umma suke ta barci.
Kamar yadda aka gani a cikin wani faifan bidiyo, faston ya ga shigowar wasu tsageru rike da bindiga cocinsa a lokacin da yake kan mimbari yana wa'azin Lahadi.
Kwanaki kaɗan bayan kashe malamin cocin Katolika a Kaduna, wasu miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da wani Fadan Katolika a garin Tambuwal da ke jihar Sokoto.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari