Harin jirgin Abj-Kad: 'Yan bindiga sun sako 3 cikin 62 da suka sace, suke azabtarwa

Harin jirgin Abj-Kad: 'Yan bindiga sun sako 3 cikin 62 da suka sace, suke azabtarwa

  • Yanzun nan 'yan bindiga suka sako mutum uku daga cikin wadanda ke hannunsu na fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
  • A jiya ne 'yan bindigan suka fitar da wani bidiyo da ke nuna lokacin da suke yi wa fasinjojin bulala a cikin wani daji
  • 'Yan bindiga sun yi barazanar sace shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai

Abuja - 'Yan ta'adda sun sako mutane uku cikin fasinjojin 62 da suka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

Wadanda aka sakon sun hada da maza biyu da mace daya, sun kuma samu ‘yancinsu ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin.

Gidan Talabijin na Channels ya tattaro cewa ‘yan ta’addan sun sako su ne a wani wuri da ke tsakanin dajin da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Daga nan 'yan uwansu suka karbe su.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ma'aikatar ilimi ta ba da umarnin garkame makarantun gwamnatin tarayya na Abuja

'Yan bindiga sun sako mutum 3 cikin 62 da ke hannunsu
Harin jirgin Abj-Kad: 'Yan bindiga sun sako 3 cikin 62 da suka sace, suke azabtarwa | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake tsokaci ga jaridar Daily Trust game da sakin su, wani mawallafi na Kaduna, Tukur Mamu, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Eh an saki uku cikin wadanda aka sace, mace daya da maza biyu. Amma ku tuna fa ba na cikin tattaunawar da ta kai ga samun ‘yancinsu."

Ya zuwa yanzu, mutane 22 da abin ya shafa ne suka samu 'yancinsu, idan aka hada da wadanda aka sako a baya.

Sai dai ba a bayyana ko an biya wa 'yan ta'addan wani kudi na fansa ba domin su sako mutanen uku.

Yayin da aka sako mutanen uku da aka yi garkuwa da su, ya zuwa yanzu adadin wadanda ke hannun tsagerun ya rage 40.

Yadda lamarin ya faro

A ranar 28 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka dasa bam a titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da fasinjoji da dama, lamarin da ya yi kamari ya fusata 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

A lokacin, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya ta dakatar da ayyuka na wani dan lokaci, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin tsaro da su ceto wadanda lamarin ya shafa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne 'yan ta'addaN suka fitar da wani faifan bidiyo inda aka gansu suna jibgar mutanen. Sun kuma yi barazanar sace shugaba Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Fadar shugaban kasar dai ta mayar da martani ga wannan barazana sa'o'i bayan da ta zargi 'yan tada kayar bayan da amfani da farfaganda don tilasta gwamnati wajen biyan bukatarsu.

Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai A Sabon Bidiyo

A tun farko, 'yan makonni bayuan farmakin da aka kaiwa ayarin motocin shugaba Muhammadu Buhari a jihar Katsina, yan ta’adda sun yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasar na Najeriya.

An dai farmaki tawagar tsaron shugaban kasar a hanyarsu ta zuwa mahaifar Buhari da ke Daura gabannin bikin Sallah. Mutane biyu sun jikkata a harin wanda aka ce fadar shugaban kasar ta dakile.

Kara karanta wannan

Bidiyon azabtarwa: Iyalan Fasinjojin jirgin ƙasa sun mamaye ma'aikatar Sufuri a Abuja, sun hana kowa shiga, Hotuna

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, a cikin sabon bidiyon da suka saki, yan bindigar wadanda suka sace fiye da fasinjoji 60 a jirgin kasar Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar sacewa da kuma halaka Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel