Ina tausaya wa sauran da ke hannun yan ta'adda, Fasinjan jirgin ƙasa da ya kubuta ya magantu

Ina tausaya wa sauran da ke hannun yan ta'adda, Fasinjan jirgin ƙasa da ya kubuta ya magantu

  • Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna da suka samu kubuta jiya ya ce yana tausayawa ragowar da ke hannun yan ta'adda
  • Hassan Usman, wanda ya kasance lauya, ya bayyana yadda rayuwarsu ta kasance a sansanin yan ta'adda
  • A cewarsa sun fara bugun su ne saboda halin da gwamnati ta nuna lokacin da aka yi yunkurin kuɓutar da su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Hassan Usman, wani lauya kuma ɗaya daga cikin waɗan da yan ta'adda suka sace a harin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja, ya ce yana tausayawa ragowar fasinjojin da ke hannun yan bindiga.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ya faɗi haka ne saboda azabtarwan da yan ta'adda ke musu waɗan da ake tsammanin mayakan kungiyar ISWAP ne.

Usman, yayin wata hira da sashin Hausa na BBC, ya bayyana godiyarsa mara iyaka ga Allah SWA bisa amincewarsa har ya samu kuɓuta.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yan bindiga sun yi wa sojoji kwantan ɓauna, sun buɗe musu wuta a Abuja

Fasinjojin jirgin ƙasa.
Ina tausaya wa sauran da ke hannun yan ta'adda, Fasinjan jirgin ƙasa da ya kubuta ya magantu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Fasinjan wanda ya shaƙi iskar yanci yana ɗaya daga cikin waɗan da suka yi jawabi a sabon Bidiyon da ya bayyana, inda suka roki majalisar ɗinkin duniya, Birtaniya da sauran ƙasashen duniya su sa hannu a saki sauran fasinjojin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, a ranar Jummu'a, iyalan waɗan da aka yi garkuwa da su sun yi yunkurin ceto su amma gwamnati ta ƙi yarda su cimma nasara.

Ya ƙara da cewa wani yunkuri da iyalan suka ƙara yi ranar Litinin ya yi nasara, wanda ya kai ga kubutar wasu mutum uku.

Usman ya ce:

"Gwamnati ta gaza samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin yan ƙasa, ya gaza ceto mu, ban sani ba ko an biya kuɗin fansa kamin su sako mu. Lokacin da ruwa ya fara sauka sun gina mana rumfa, suna ciyar da mu yadda tsarin su yake."

Kara karanta wannan

Daya Daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa Da Aka Saki, Barista Hassan Ya Sadu Da Yan Uwansa A Bidiyo

"Wani lokacin suna yanka shanu ko tumaki domin mu, ko jiya sun yanka mana Sa kuma mun ci nama, Mun gode Allah. Saboda halin da gwamnati ta nuna sun fusata shi ne suka duke mu."
"Sun duke mu ba imani kuma wannan ne somin taɓi, hakan ya sa nake tausaya wa ragowar waɗan da ke can daji tare da su."

A wani labarin kuma Gwamna Zulum ya raba tsabar kuɗi miliyan N172m da abinci ga talakawa 30,436 a karamar hukuma ɗaya

Gwamnan jihar Borno ya tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa da masu karamin karfi a yankin Damboa.

Farfesa Babagana Umaru Zulum ya sa ido wajen raba tsabar kudi miliyan N172m da kayayyakin abinci ga mazauna 30,436.

Asali: Legit.ng

Online view pixel