Labaran garkuwa da mutane
Tawagar IRT dake karkashin sifeta janar na 'yan sanda, ta damke mai kai wa 'yan bindiga bayanan da ya kai ga sace mata da 'ya'ya 2 na 'dan majalisa a Katsina.
An ce tsagrun sun yi bindige wani soja tare da yin awon gaba da wasu jami’an kamfanin gonar mutum biyu da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba 24 ga watan Agusta.
Za a ji yadda aka yi garkuwa da Sarki da ‘Yan fadarsa a Ribas. Tun da aka yi gaba da Sarkin na karamar hukumar Akuku Toru a Ribas, ba a sake jin duriyarsa ba.
Yayin da'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa game da mulkin Buhari, tsohon gwamnan Bauchi ya yaba da irin kokarin da Buhari ya yishekarun mulkinsa na Najeriya.
Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya yaba da irin kokarin da shugaba Buhari ya yi na kare 'yan Najeriya da dukiyoyinsu baki daya.
Manoma a kananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi a jihar Neja sun shiga damuwa yayin da suke fara shirin girbin amfanin gonakansu a halin yanzu da ake girbi.
Yan sanda sun yi ram da wani mutum wanda da bakinsa ya amsa cewa yana neman yadda zai kashe Yakubu Dogara. Kwamishinan Yan Sanda na Bauchi ya bayyana wannan.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya magantu kan batun da ya shafi tsaron Najeriya, ya kuma bayyana cewa shi dai ya san mafita gareta cikin sauki.
A jiya Asabar 20 ga watan Agusta ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC mutum biyu tare da kashe wasu uku a jihar Imo a Kudu.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari