Mazauna Kauyuka Ke Taimakawa ’Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane, Inji Gwamna Bello Masari

Mazauna Kauyuka Ke Taimakawa ’Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane, Inji Gwamna Bello Masari

  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya zargi mazauna yankunan Katsina da taimakawa 'yan ta'adda a jihar
  • A zarginsa, ya ce ana garkuwa da mutane ne aikata sauran ayyukan barna tare da taimakon bayanai daga mazauna
  • Gwamnan, ya kuma yi kira ga al’ummar jiharsa da su ba jami’an tsaro hadin kan ragargazar 'yan ta'adda a jihar

Jihar Katsina – Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bayyana zarginsa ga mazauna kauyuka da ke kewayen jihar da ba 'yan ta'adda bayanan sirri domin aiwatar ayyukan ta'addanci.

Ya yi wannan zargin ne a ranar Talata 30 ga watan Agusta yayin kaddamar da motocin sulke bugun Najeriya guda tara da aka ba jami’an tsaro domin yaki da matsalar rashin tsaro a Katsina, inji rahoton This Day.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: ‘Yan Gari Sun yi Wa Shugaban Karamar Hukumarsu Ruwan Dutse

Masari ya kuma koka da yadda ‘yan ta’adda ke kara karfi bayan wasu hare-hare da suka rika kaiwa wasu kauyuka a fadin jihar.

Gwamna Masari ya gano masu ta'azzara matsalar tsaro a Katsina
Mazauna kauyuka ke taimakawa 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane, inji Gwamna Bello Masari
Asali: Facebook

Ya ce akwai bukatar a dakile motsi da karfin tsageru tare da fatattakarsu don tabbatar an dakile ayyukan su a fadin jihar baki daya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masari ya ce:

“Da dannan motoci tara, muna da motocin sulke na APC sama da 30 kenan a Katsina, domin tunkarar ‘yan bindigan da suka addabe mu, musamman a yankunan gwamnatin jihar.”

Za mu tabbatar da kawo karshen 'yan ta'adda gaba daya, inji Masari

Gwamnan ya kuma bayyana kwarin giwarsa ta murkushe 'yan ta'adda tare da daidaita lamrran tsaro a jihar kafin karshen gwamnatinsa.

Sai dai, ya ce hakan ba zai yiwu ba har sai mazauna jihar sun taimakawa jami'an tsaro ta hanyar ba su hadin kai da kuma ba su bayanan sirri game da 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: ASUU ta gama tattaunawa a Abuja, ta sake fitar da matsaya

Gwamnatin jihar ta ba da tallafin motocin ne domin kawo lamurran tsaro a jihar, rahoton Leadership.

Jerin Kananan Hukumomi 40 a Najeriya da Ba Lallai a Yi Zabe Ba a 2023

A wani labarin, ta'azzarar rashin tsaro a Najeriya ya sa 'yan kasar da dama cikin tashin hankali, kuma kullum tsoro karuwa yake a zukatan wasu da dama.

Jaridar Punch, ta ruwaito cewa, akwai kananan hukumo sama da 40 da ba lallai su kada kuri'u ba a zabe mai zuwa saboda yawaitar harin 'yan ta'adda.

Kananan hukumomin 40 suna karkashin fadin jihohin Kaduna, Zamfara, Niger, Katsina, Abia da Imo ne, kuma ga su kamar haka:

Asali: Legit.ng

Online view pixel