'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sojojin Najeriya, Sun Kashe 2, Sun Jikkata 4 a Katsina

'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sojojin Najeriya, Sun Kashe 2, Sun Jikkata 4 a Katsina

  • Wani mummunan lamari ya faru a jihar Katsina, sojojin Najeriya biyu sun rasa rayukansu yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki
  • Akalla sojoji hudu ne suka jikkata yayin da wani bam ya tashi da wata motar sulke ta soja da tsagerun suka farmaka
  • Ana yawan samun hare-haren 'yan bindiga a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya, lamarin da ke kara tsoro tsakanin mazauna

Shimfida, jihar Katsina - Yanzu muke samun labarin cewa, wasu tsagerun ‘yan ta’adda sun yi wa motar sulke ta sojin Najeriya kwanton bauna, inda suka hallaka sojoji sojoji biyu tare da raunata wasu hudu a yankin Shimfida dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Jaridar This Day ta ce ta samo daga majiya cewa, an yi wa sojojin kwanton bauna ne da misalin karfe 10 na safe yayin da suke raka wasu jama'a zuwa garin Jibia domin siyo kayan abinci.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Gwamnan APC Ya Umurci Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Kamo Masa Wani Sarki A Jiharsa

Yadda 'yan bindiga suka farmaki sojoji a Katsina
'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sojojin Najeriya, Sun Kashe 2, Sun Jikkata 4 a Katsina | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Majiyar ta kuma ce, sojojin da aka kashe na daga cikin dakarun bataliya ta 32 ta sojojin Najeriya da aka tura Shimfida dake fama da barnar 'yan bindiga.

Ta kuma kara da cewa, motar sojin ta yi karo ne da nakiyar IEDs ta 'yan ta'addan suka dasa a hanyar ta Shimfida zuwa Gurbi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, ya ce sojojin biyu sun mutu ne nan take, yayin da hudun kuwa suka samu raunuka daban-daban lokacin da bam din ya tarwatse, haka nan Daily Nigerian ta ruwaito.

A bangare guda, ya ce an nemi wani laftana mai suna Musa da ya bace bayan hari, har yanzu ba a gan sa ba.

Mazauna Kauyuka Ke Taimakawa ’Yan Bindiga da Masu Garkuwa da Mutane, Inji Gwamna Bello Masari

A wani labarin, gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bayyana zarginsa ga mazauna kauyuka da ke kewayen jihar da ba 'yan ta'adda bayanan sirri domin aiwatar ayyukan ta'addanci.

Kara karanta wannan

Gidan soja: Yadda yunwa ta kashe sojojin Kudancin Sudan sama da 200 a cibiyoyin horon soji

Ya yi wannan zargin ne a ranar Talata 30 ga watan Agusta yayin kaddamar da motocin sulke bugun Najeriya guda tara da aka ba jami’an tsaro domin yaki da matsalar rashin tsaro a Katsina, inji rahoton This Day.

Masari ya kuma koka da yadda ‘yan ta’adda ke kara karfi bayan wasu hare-hare da suka rika kaiwa wasu kauyuka a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.