Iyalin Tukur Mamu Sun Bada Labarin Yadda DSS Suka Shigo Dakin Matansa Cikin Dare

Iyalin Tukur Mamu Sun Bada Labarin Yadda DSS Suka Shigo Dakin Matansa Cikin Dare

  • Bayan an cafke Tukur Mamu, sai ga labari cewa dakarun DSS sun yi motoci zuwa gidan ‘dan jaridar a Kaduna
  • Ana kwance sai iyali suka ji ma’aikatan tsaro masu fararen kaya sun dura gida da ofishin Malam Tukur Mamu
  • Wani na-kusa da mawallafin ya zargi DSS da ci masu zarafi da sunan bincike, ba tare da kotu ta bada umarni ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Iyali da ‘yanuwan Malam Tukur Mamu sun bayyana cewa sun kidime a sakamakon shigo masu gida da hukumar DSS suka yi a garin Kaduna.

Wani ‘danuwan Malam Tukur Mamu ya shaidawa Daily Trust cewa dakarun DSS sama da 50 suka shigo gidansu cikin motoci kimanin 20 a daren Alhamis.

Jami’an tsaron na fararen kaya sun isa gidan Tukur Mamu da ke Unguwar Dosa a jihar Kaduna da kusan karfe 12:30am, a lokacin kusan kowa ya kwanta.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu, Sun Kwashe Kwamfuyutoci da Takardu

Kamar yadda suke aiki, jami’an tsaron sun yi wa gidan kaca-kaca, suka lalube ko ina. ‘Danuwan wannan mutumi yace shigowar rundunar ne ya farkar da su.

An zo babu takardar kotu

Majiyar tace jami’an sun zo ne dankare da makamai, kuma yace ba a nuna masu takardar da ta bada dama su shigo gidan da sunan za su yi bincike ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An rahoto ‘danuwan mawallafin yana cewa ba a iya samun komai ba, amma abin ya tada masu hankali.

DSS..
Ma'aikatan DSS Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Haka kuma an samu labari jami’an sun tursasawa daya daga cikin ‘ya ‘yan Hadimin na Sheikh Abubakar Gumi ya yi irin sa hannun mahaifinsu a takarda.

Kamar yadda ‘danuwan ya fadawa manema labarai yau da safe, ba a ba yaron damar karanta abin da takardar ta kunsa ba, amma aka matsa ya sa hannu.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 da ya Dace a Sani Game Da Tukur Mamu, Hadimin Gumi da DSS Suka Kama

An shiga dakin matan Tukur Mamu

Idan maganarsa ta tabbata, dakaraun sun burma har dakin matar mai gidan jaridar na Desert Herald, wanda hakan ya ci karo da tsarin addinin musulunci.

Karfa-karfan da aka yi ya sa ‘danuwan ya yi kira ga jama’a su tashi tsaye domin ayi tir da wannan aiki. A cewarsa, an saba doka, an keta masu alfarmarsu.

Legit.ng Hausa ta tuntubi wani makwabcin wannan mutumi, wanda ya shaida mata cewa jami'an tsaron ba su bar gidan ba sai kusan lokacin sallar asuba.

Majiyar ta bayyana mana cewa an yi gaba da duka wayoyin wadanda aka samu a gidan. Baya ga haka, mun ji labari an saki matan wannan Bawan Allah,

Premium Times tace an dauke komfutoci da wayoyin salula da aka samu a ofis da gidan Malam Mamu, kuma har yanzu mai gidan da wasu iyalin na tsare.

Wanene Tukur Mamu?

Kafin yanzu kun ji cewa Tukur Mamu Mazaunin Kaduna ne kuma mawallafin jaridar Desert Herald, yana rike da sarautar 'dan Iyan Fika a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan ta'adda suka farmaki yankin Kaduna, sun sace mutane, sun kashe wasu

Mamu shi ne wanda ya jagoranci sasanci tsakanin 'yan ta'adda da iyalan fasinjojin jirgin kasa da aka sace a kan hanyarsu ta dawowa Kaduna daga Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel