Asiri ya tonu: Tsohon Shugaban Sojojin Najeriya Ya Sace Naira Biliyan 4 - ICPC

Asiri ya tonu: Tsohon Shugaban Sojojin Najeriya Ya Sace Naira Biliyan 4 - ICPC

  • Farfesa Bolaji Owasanoye yace akwai hannun wasu jami’an tsaro wajen matsalolin da ake fuskanta
  • Shugaban hukumar ICPC ya yi jawabi a wani taro da aka yi a Abuja, ya tona yadda manyan sojoji ke barna
  • Bolaji Owasanoye ya bada labarin wani hafsun soja wanda ya saci N4bn daga gidan sojoji, ya saye gidaje

Abuja - Shugaban hukumar ICPC ta kasa, Bolaji Owasanoye ya koka a kan yadda jami’an tsaro suke aikata rashin gaskiya, a maimakon su kawo zaman lafiya.

This Day ta rahoto Farfesa Bolaji Owasanoye yana cewa akwai wani tsohon shugaban hafsun sojoji a Najeriya da ake zargin ya yi gaba da Naira Biliyan hudu.

Shugaban na ICPC yace wannan tsohon jami’in tsaro ya saci dukiyar ne daga kasafin kudin sojoji, ya boye su a cikin wasu kamfanoni da shi kadai ke da iko da su.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

Owasanoye yace a karshe an yi amfani da kudin satar a wajen mallakar gidaje a Abuja ta hanyar amfani da sunayen wasu daban domin gudun hukuma ta gane.

Daga baya tsohon jami’in tsaro ya dawo yana amfani da kadarorin da aka mallaka da sunan wani.

ICPC tayi taro a Abuja

Rahoton Punch ya tabbatar da cewa Farfesan ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro da aka shirya a kan satar dukiyar kasa da kuma rashin tsaro a Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

ICPC.
Shugabannin ICPC Hoto: icpc.gov.ng
Asali: UGC

Farfesa Owasanoye yake fadawa wadanda suka halarci zaman cewa binciken NSA da ICPC ya nuna jami’an gwamnati suna da hannu a matsalar rashin tsaro.

Muna binciken tsofaffin sojoji - ICPC

"ICPC da ‘yaruwarmu EFCC suna binciken wasu tsofaffin jami’an tsaro da sojoji bisa zargin facaka da kudin da aka ware domin matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

Misali akwai wani tsohon shugaban wani bangare na sojoji, a lokacin mulkinsa, ya tura N4bn daga kasafin kudin sojoji zuwa kamfanoni biyu
Shi kadai ya mallaki wadannan kamfanoni, kuma shi kadai yake da ikon sa hannu.
An yi amfani da kudin wajen sayen kadarori a Abuja da sunan wasu mutane dabam. Wasu kadarorin da aka mallaka, sun dawo hannusa.

Za a cigaba da shari'a a kotu

Da aka je kotu, Alkali ya karbe wasu cikin kadarorin amma ya bar wasu, Owasanoye yace ICPC za ta daukaka kara, domin karbe duk ragowar kadarorin.

An gudanar da wannan taro ne a karshen makon jiya a hedikwatar ICPC da ke garin Abuja. A zaman, an tabo batun yadda ake saida guraben samun aiki.

ASUU v FG

Kuna da labari shugaba Muhammadu Buhari na neman tursasawa malaman jami’a su koma aiki, an shigar da karar kungiyar ASUU a kotun NIC a Abuja.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

An fahimci ‘Yan kungiyar ASUU a Najeriya sun yi tanadin gawurtattun Farfesoshi da Lauyoyi kusan 50 da za su kare su, ba tare da an biya su sisin kobo ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel