Lauya Falana Ya Maka Buhari da Wasu Mutane a Kotu Saboda Harin da Aka Kai Magarkamar Kuje

Lauya Falana Ya Maka Buhari da Wasu Mutane a Kotu Saboda Harin da Aka Kai Magarkamar Kuje

  • Lauya a Najeriya ya bayyana maka shugaban kasan Najeriya a kotu saboda harin da aka kai gidan gyaran hali na Kuje
  • A watan Yulin bana ne wasu 'yan ta'adda suka kai mummunan hari gidan gyaran hali na Kuje, suka saki fursunoni
  • 'Yan Najeriya sun shiga firgici ganin yadda 'yan ta'adda suka kutsa babban birnin kasar kuma suka tafka barna

Jihar Legas - Lauya kuma dan rajin kari hakkin bil'adama, Femi Falana (SAN) ya maka shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari a kotu kan wani harin da ‘yan bindiga suka kai magarkamar Kuje dake Abuja a watan Yulin bana.

A yayin harin da ya tada hankalin 'yan Najeriya, 'yan ta'addan sun saki fursunoni sama da 600, ciki har da wasu rikakkun 'yan ta'addan Boko Haram 64, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Manyan 'Yan Siyasa 10 Masu Karfin Tasiri a Zabukan 2023 Dake Gabatowa

Lauya Falana ya maka Buhari a kotu
Lauya Falana ya maka shugaba Buhari da wasu mutane a kotu saboda harin da aka kai magarkamar Kuje | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Falana ya shigar da karar ne ta hannu lauyoyinsa da suka hada da Misis Funmi Falana da Adeola Ademuwagun a ranar 23 ga watan Agusta a babbar kotun tarayya dake Legas.

Wadanda ake kara na daya zuwa na uku sun hada da shugaban kasa, majalisar dokokin kasa da kuma babban kontrolan hukumar gyaran fuska ta Najeriya, Premium Times.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jerin wadanda ake kara uku sun hada da shugaban kasa Buhari, majalisar dokoki ta kasa da kuma babban kwanturola na hukumar gyaran hali ta Najeriya.

Abubuwa biyu da lauyan ya nema

Sammacin na Falana ya jawo hankalin alkali ga tambayoyi guda biyu da ya nemi a tantance su kamar haka:

  1. Shin bangarori uku da ya maka kotu ba su sanya na'uarar bin diddiga da ta dau-dauka (CCTV) da sauran kayan aikin kare cibiyar gyaran halin bane, kamar yadda sashe na 28 (2) na dokar Hukumar Kula da Gyaran Halin Najeriya ta tanada.
  2. Shin me ya hana wadanda yake kara uku su samar da isassun dakaru da jami'an tsaron da za su dakile hare-hare a gidan gyaran halin, kamar yadda sashe na 28 (2) na dokar Hukumar Kula da Gyaran Halin Najeriya ta tanada.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 3 Dake Kaiwa 'Yan Bindiga Bayanan Sirri

Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dakta Sadiq

A wani labarin, Dakta Sadiq Amali na sashin nazarin halayar mutane a Jami'ar Tarayya ta Jigawa ya bayyana cewa ya yi hasashen za a kai hari gidan yarin Kuje a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Yayin da ya ke magana kan harin a shirin Sunrise Daily na Channels TV, Dakta Amali ya ce ya rubuta wasika ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbsola, game da yiwuwar kai harin.

Yan bindiga da ake kyautata zaton yan ta'adda ne, daruruwansu sun kai hari gidan yarin a ranar Talata da dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel