‘Yan Sanda Sun Cafke Likita Mai Yin Allurar Mutuwa, Ya Sace Motocin Marasa Lafiya

‘Yan Sanda Sun Cafke Likita Mai Yin Allurar Mutuwa, Ya Sace Motocin Marasa Lafiya

  • Ana zargin wani Likita a asibitin Kaiama da ke Arewacin jihar Kwara da laifin kashe marasa lafiyansa
  • Idan Likitan ya kashe marasa lafiya ta hanyar allura, ya kan dauke motocinsu domin ya saida a kasuwa
  • Dubun wannan mutumi da ake zargi ta cika bayan an gano wata mota da ya saida bayan ya kashe mai ita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Edo - Jami’an ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Edo, sun yi ram da wani likita da ake zargin yana da hannu wajen mutuwar wasu direbobin mota.

Premium Times tace wannan likita mai suna Abbas Adeyemi yana yi wa marasa lafiya muguwar allurar da take yin kisa, domin ya sace motocinsu.

Abbas Adeyemi mai shekara 36 yana aiki ne a babban asibitin garin Kaiama a jihar Kwara.

Likitan ya amsa laifinsa, ya fadawa dakarun ‘yan sanda cewa ya sace motoci biyu daga hannun wasu marasa lafiyansa bayan ya tsira masu allura.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: Abubuwan da Zan Yi a Kwanaki 100 na Farko da Zan Yi a Ofis

Kamar yadda kakakin ‘yan sanda na jihar Edo, Chidi Nwabuzor ya bayyana a jiya, Adeyemi mutumin garin Offa ne a Kwara, yana da ‘ya ‘ya biyu.

Likita ya kashe Emmanuel Yobo

Wannan likita ake zargi da laifin kashe wani direban mota, Emmanuel Yobo mai shekara 39 a farkon watan Satumban nan, bayan ya yi masa allura.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan Sanda
Wani 'Dan Sanda Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Likitan ya fadawa jami’an tsaro cewa ya tsirawa Emmanuel Yobo wasu sinadarai masu hadari, ‘yan sanda suka ce wannan ya yi sanadiyyar ajalinsa.

Bayan ya yi masa wannan allura kuma ya mutu ne sai likitan ya jefar da gawar wannan bawan Allah a kan titin Benin-Ondo, ya dauke motarsa.

Kamar yadda rahoton ya tabbatar, Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Edo yace likitan ya yi nasarar dauke motar marigayin, kirar Toyota Camry.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

Da dakarun ‘yan sanda masu binciken garkuwa da mutane da ‘yan damfara suka shiga aiki, an gano motar a garin Osogbo, daga nan aka kamo likitan.

Wanda ya saye motar da aka sace ya fadawa ‘yan sanda cewa ya taba sayen wata mota da likitan ya kawo masa da ya kashe wani mutumi a Kwara.

Hafsun Soja ya sace kudin tsaro

Kwanaki kun ji labari wani Hafsun Soja da aka yi a Najeriya, ya yi amfani da damar ofishinsa, ya sace Biliyoyin kudi domin ya mallaki kadarori a Abuja.

Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye yace hukumarsa tana binciken barnar da wasu miyagun jami’an tsaro suke yi, maimakon kawo zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel