‘Yan Bindiga Na Neman N10m na Fansar Gawar Wanda Suka Yi Garkuwa Dashi

‘Yan Bindiga Na Neman N10m na Fansar Gawar Wanda Suka Yi Garkuwa Dashi

  • Wasu miyagun ‘yan bindiga sun sace wani mutum tare da halaka shi sannan suke neman kudin fansa har N10 miliyan daga ‘yan uwansa kafin su saki gawarsa
  • Kamar yadda ‘dan uwan mamacin ya bayyana, an sace ‘dan uwansu a kan hanyarsa ta Abuja zuwa Kaduna kuma sun biya N3 miliyan da babur daya na fansa
  • Ya sanar da cewa ‘yan bindigan sun ce ‘yan sanda sun halaka wasu daga cikinsu don haka suka huce fushinsu ta hanyar harbe shi, amma sai sun biya kudi zasu saki gawar

Kaduna - ‘Yan bindiga sun bukaci a basu N10 miliyan matsayin kudin fansa kafin su saki gawar wani wanda suka yi garkuwa da shi mai suna Obadiah Ibrahim a makonni kadan da suka gabata a Kaduna.

Taswirar jihar Kaduna
‘Yan Bindiga Na Neman N10m na Fansar Gawar Wanda Suka Yi Garkuwa Dashi. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa, ‘dan uwan wanda aka sace mai suna Kefas Obadiah, yace ‘yan bindigan sun karba N3 miliyan amma sun ki sakin gawarsa bayan sace shi da suka yi a watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Adamawa: Jami’an ‘Yan Sanda Sun Cafke Matashi da Ake Zargi da Damfara da ATM 10

“Ibrahim ya rasa ransa a ranar Litinin kuma sun sanar mana ranar Alhamis. Mun bukaci gawarsa amma sai suka ce sai mun biya N10 miliyan idan muna son gawarsa don ba zasu yi mana aiki kyauta ba.”

- Yace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya kasance

Obadiah yayin bayanin halin da suka fada ya kara da cewa:

“Sunan ‘dan uwana Obadiah Ibrahim. An yi garkuwa da shi a farkon watan Oktoba a Sabon Gaya yayin da yake hanyarsa daga Abuja zuwa Kaduna.
“Duk da ba da ni ‘yan bindigan ke magana ba, akwai wanda suke cinikin da shi. A farko sun bukaci N200 miliyan kuma daga baya aka daidaita a N3 miliyan da doriya.”

Ya kara da cewa:

“Sun ce mu je mu kawo kudi. Bayan mun basu kudin fansa, sun ce na kudin kayan abincinsu ne wanda ya kare don haka mu je mu karo N15 miliyan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Fitattun Malamai Biyu a Jihar Arewa

“Daga bisani suka yi kasa inda suka ce mu kawo N5 miliyan da babura uku kuma daga baya suka karba babur daya. Bayan karbar babur din bamu ji daga wurinsu ba. Mun yi kokarin ji daga wurinsu amma shiru.
“Sai a ranar Alhamis yayin da wanda suke cinikin dashi ya kira su, sun ce ‘dan uwanmu ya mutu. Mun zata wasa suke. Amma sai da muka cigaba da kiransu sai suka yi barazanar bibiyarsa su kama shi shima idan bai daina kiransu ba.”
“Sun ce ‘yan sanda sun kama wasu daga cikinsu, sun daure su a bishiya tare da kashesu. Don haka suka sauke fushinsu a kan ‘dan uwanmu.
“‘Yan bindiga sun yi rantsuwa da Allah cewa idan muka kawo kudin zasu saki gawar a cikin kwanaki uku.”

- Ya cigaba da cewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel