'Yan Sanda Sun Kama 'Yan Bindiga 16 da Masu Garkuwa Da Mutane a Zamfara

'Yan Sanda Sun Kama 'Yan Bindiga 16 da Masu Garkuwa Da Mutane a Zamfara

  • Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta bayyana kama wasu 'yan ta'adda da suka addabi al'ummomin jihar
  • An kama kasurguman 'yan bindiga da masu fashi da makami da kuma masu kitsa sace-sace a zagayen jihar
  • A makon nan an hallaka wasnu 'yan ta'adda da dama a yankin Kaduna a ayyukan kakkabe 'yan ta'adda a Arewa maso Yamma

Gusau, jihar Zamfara - Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta kama wasu 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da 'yan fashi 16 a aikin da jami'ai ke yi na kakkabe yankin Arewa maso Yamma daga ayyukan 'yan ta'adda.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mohammed Shehu ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da tsagerun ga manema labarai a madadin kwamishin 'yan sandan jihar Kolo Yusuf.

Ya kuma bayyana cewa, 'yan sanda ne suka kamo 'yan ta'addan a yankuna daban-daban na jihar, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Luguden NAF Ya Halaka Manyan Yan Bindiga 3 da Ake Nema da Mayankansu a Jihohin Arewa

An kama 'yan bindiga a Zamfara
'Yan Sanda Sun Kama 'Yan Bindiga 16 da Masu Garkuwa Da Mutane a Zamfara | Hotuna: channelstv.com
Asali: UGC

Wadanda aka kama da inda aka kamo shi

Ya bayyana cewa, an kamo rikakkun 'yan bindiga, Surajo Almandawi da Bage Muhammad a kan titin Gusau zuwa Funtua.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, 'yan ta'addan su ne suka addabi yankunan Kotarkwashi, Damba da sauran kauyuka da ke zagayen garin Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce jami'ai sun kamo su ne bayan samun bayanan sirri kan barnar da suke a yankunan.

Shehu ya kuma bayyana cewa, jami'ai sun kama wani Kabiru Idi mai shekaru 35, wani Dan-Hauwa Kalla mai shekaru 31 da Majami Iliya mai shekaru 27 bisa laifin garkuwa da mutane da kashe wani yaro mai shekaru 6 bayan karbar kudin fansa.

A bangare guda, wasu jami'an da suka shigan bultu sun kama wasu barayin mota uku, inda aka gano karamar bindiga da mota kirar Hyundai guda daya, kuma sun amsa laifinsu, Radio Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari ya shiga tashin hankali bisa kashe wani basaraken gargajiya a wata jiha

An kwato kayayyaki, an kama barayi

Hakazalika, wasu jami'ai sun yi nasarar dakile harin da aka kai yankin Dan Sadau na karamar hukumar Maru, inda suka kwato bindigogi kiran AK-47 guda byu da alburusai 35.

Daga karshe SP Shehu ya ce, an kama wani Bello Mohammed mai shekaru 4o na Gadar Bage a Gusau bisa zargin kitsa wata sata a yankin.

An kuma kwato kayayyakin aikata laifuka da dama, ciki har da wani busasshen ganye, kamay yadda rundunar ta bayyana.

A makon nan kuma sojoji suka yi nasarar bindige tsagerun 'yan bindiga; Kachalla Gudau da Rigimamme a yankunan jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel